✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lafiyar Dabbar Layya

Likita me zai iya faruwa na matsalar lafiya ga wadanda suka ci naman dabba maras lafiya? Amsa: Kiwon lafiyar dan Adam ba ta cika har…

Likita me zai iya faruwa na matsalar lafiya ga wadanda suka ci naman dabba maras lafiya?

Amsa: Kiwon lafiyar dan Adam ba ta cika har sai lafiyar cimakarsa ma ta zamanto ingantacciya. A cikin abubuwan da mukan ci yau da kullum har da naman dabbobi musamman mu anan galibi raguna ne, da awaki da shanu. Sai ga shi kuma cewa lokaci ya zo da za a kara yawan hulda da naman wadannan dabbobi. A addinance kowa ya san dabba wadda ba lafiyayya ba ba ta layya. Haka ma a likitance, dabba mai ciwo ba a cinta ko da wane lokaci ne, har sai likitocin dabbobi sun dubata sun tabbatar da cewa za a iya ci, sabanin yadda wasu da dama kan sayar mana da dabbobi wadanda suka ‘kasa’. Abinda watakila ya sa aka ce kada a yanka maras lafiya din kenan, ko gurguwa ko mai ido daya ko mai wata nakasa. Wato domin kai mai saye ba ka san takamaimai wane ciwo ne ya nakasa ta ba, kuma watakila don kada mutane su dauki ciwon, tunda cutuka kan nakasa mutum da dabba. Ko a mutane akwai cutuka da dama masu sa gurguntaka (kamar kwayar shan inna) da sauran ire-iren nakasa.

Rashin lafiya iri-iri ne kan iya kama dabbobin da mukan ci, kuma da dama cutukan da kan kama su din za mu iya dauka idan muka ci naman dabbar mai cutukan. Wadannan cutuka da muka fi dauka daga dabbobi yawancinsu sanadinsu kwayoyin cuta ne. Wato kwayoyin cuta za su iya shiga jikinmu ta hanyar naman da muka ci wanda ba mai lafiya ba ne. Babban misali shi ne kwayoyi ko kwayayen macizan ciki da muke kwasa daga wadannan dabbobi, sai kwayoyin cutuka irin na bacteria da protozoa masu sa mana zawo (E.coli) idan mun ci nama a wasu lokuta, ga irinsu ciwon typhoid da kwayar hepatitis wadda ke iya lalata hanta. A makon da ya gabata ne a kasar Ingila aka ba da sanarwar bullar cutar hepatitis ta rukunin E a wasu dabbobi da aka yanka aka kai manyan shagunan sayar da kayan abinci, inda ake ganin mutane da dama za su iya kamuwa.

Wannan a kasar da akwai dokokin kiyaye lafiyar dabbobi ma kenan. To mu ma idan ba ma kiyaye lafiyar dabbobinmu to tabbas za a iya samun bullar cutuka a mutane wadanda dabbobi sukan sa mana. Sai dai abin kwantar da hankali game da wannan batu shine cewa kusan mu a kasar nan ana dafa nama sosai kafin a ci, sabanin irin kasashen Turai da kan ci nama danye-danye. Yawanci inda aka fi kamuwa da cutukan a nan sune a wajen rashin iya tsabtace naman da wanke shi sosai kafin a ci, kamar wanke kayan ciki, irinsu tumbi da hanji, inda kusan nan ma matattara ce ta kwayoyin cutaka iri-iri.

Yawanci dabbobin na kwasar wadancan cutukan ne tun daga wurin kiwo, inda wasu kan sake su su yi ta cin abinda suka ga dama, wanda a nan ne suke cin kwayoyi da kwayayen cutuka daban-daban. Sai kuma wurin yanka. Babu wanda zai shiga mayanka a manyan garuruwanmu hankalinsa bai tashi ba saboda kazanta. A nan dabba ko ba ta da cuta saboda rashin tsabta za ta iya kwasar cutukan jini irinsu kwayar hepatitis, tunda ko ina jini ne, sabo da kuma busasshe, sannan ga kudaje ko ta ina. A mayanka kamata ya yi kada dabba ta taba kasa, kuma da an yanka ake rataye su a wuri mai sanyi. Daga mayankar kuma kusan kowa ya san ababen safarar naman dabbobin ma idan aka lura abin bakin ciki ne, a babur budadde ko bayan mota budaddiya ake safararsu kamar ba abinci ba, maimakon motoci na musamman rufaffu masu sanyi.

Don haka kenan a takaice idan mutum na so ya kiyaye kansa daga kwasar cutuka a wannan lokaci sai ya yi la’akari da duka abubuwan da aka zayyana a sama, ya tabbatar ba irin dabbobin da aka yi wa irin wancan kiwo ba ne, ya kuma tabbatar a ido ba mai alamun ciwo ba ne, ya guji kai gyara nama mayanka, ya kuma tabbata ana wanke kayan ciki sosai da sosai kafin a dora wuta, da sauran hanyoyi da ya san idan ya bi su zai inganta lafiyar namansa a wannan lokaci.

Sa’annan idan an yanka dabbar ba mutum daya ne zai sa ta a gaba ya yi ta ci shi da iyalansa ba. A’a tunda an ce dama a yanyanka a rarraba a ba mabukata, ka ga da wuya har a ce an yi cin da zai yi illa ma ga lafiya.

 

Ina yawan cin ‘ya’yan itatuwa daban daban. A sati na kan ci nau’i bakwai ko ma fiye da haka. Shin hakan yana da amfani?

Daga K. Bello, Kiyawa

 

Amsa: kwarai kuwa hakan yana da amfani musamman a irin wannan lokaci na ciye-ciyen maiko, kayan itatuwan za su iya tsane maka duk wani maiko da baya da amfani ga jikinka. Sai dai ban ji ka ambaci kayan ganye ba, don su ma suna da muhimmanci matuka kamar na itatuwan. Abinda dai kawai za a ce ka kiyaye shi ne cewa tunda ba dafa su ake ba, ka rika tabbatawa an wanke su tatas da ruwa mai tsabta kafin a ci.

 

Idan na tashi daga barci na kan ji jiri. Ko hakan matsala ce?

Daga Yahaya Darazo

 

Amsa: E, matsala ce, mun sha zayyana abubuwan da sukan jawo irin hakan. Domin sanin ko mene ne yana da kyau ka ziyarci likita a binciki dalili.

 

Me ya ke kawo kurajen da ake kira kurajen hucewar zazzabi. Na yi zazzabi sun fito mi ni su na damu na. Mece ce mafita?

Daga Ahmed, Bich

 

Amsa: Da kwayoyin cutar da suka kawo maka zazzabi da magungunan kashe zazzabi kowane a cikinsu zai iya kawo maka huciyar zazzabi. Kuma dukansu saboda su na cinye sinadaran bitaman ne na rukunin B a jikinka. Don haka idan ka samu ganyaye da kayan itatuwa ko kwayoyin bitaman ka sha na ‘yan kwanaki za su bace.