Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure, inda za mu karasa bayanin ladabi na biyar, wato zaben macen da ta dace. Da fatan Allah Ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
2. Zabar macen da ta iya soyayya: Bayan an tabbatar macen da ake da niyyar aure tana da rikon addini, sai a yi binciken ko za iya soyayyar aure? Annabi SAW Ya yi umarni ga al’ummarsa cewa:
“Ku auri masoya kuma masu haihuwa (daga mata), don in yi alfahari da yawanku ranar kiyama.
Haka kuma Ya ce:
“Ku auri budurwa, domin bakinsu ya fi zaki, kuma mahaifarsu ta fi saurin daukar ciki, sannan suna hakuri da kadan.”
Haka kuma ya ce da Sahabinsa Jabir dan Abdullah Allah Ya kara yarda a gare shi:
“Me ya sa ba ka auri budurwa ba, ka yi mata wasa, ita ma ta yi maka?”
In muka yi nazari wadannan maganganu na Manzon Allah SAW, za mu fahimci suna nuna muhimmancin zaben macen da ta iya zamantakewa mai kyau, wacce ta iya soyayya irin ta aure, kuma ta kasance mai amsar soyayyar mijinta; wacce in mutum ya aure ta, zai ji dadin zama da ita, zai yi wasa da ita, ita ma za ta yi wasa da shi, inda za su rika rige-rigen faranta wa juna rai.
Yadda ake macen da ta iya soyayya: Duk mace mai addini za a same ta da kamun kai da natsuwa, ba ta sakin fuska ga duk namijin da bai halatta gare ta ba; don haka ba a iya gane yanayin dabi’arta lokaci daya, dole sai an yi kyakkyawan nazarin yadda take zamantakewa da kawayenta da sauran mutanen da ya halatta ta saki jiki da su, kamar kannenta da mata ’yan uwa ko makwabta; in ta kasance mai saukin hali gare su, mai yi musu ayyukan sadaukarwa, mai kokarin faranta musu rai a-kai-a-kai, mai yawan yin wasa da dariya da su, mai saurin hucewa da yafewa yayin da wani abu ya shiga tsakaninsu; to wannan tana da siffofin macen da ta iya soyayya. In kuma aka yi rashin sa’a ba ta da wadannan siffofi, to sai a yi nazarin idan tana da saukin hali da kuma saurin fahimta, ta yadda bayan aure mijinta in ya mu’amulance ta da wasannin soyayya, saukin halinta zai sa nan da nan ita ma ta koya kila ma har ta fi shi iyawa. Sannan za a iya yin dubi ga mahifiyar wacce ake neman auren, idan aka tarar ta iya zamantakewar aure da mijinta, to ana kyautata zaton diyarta ma haka za ta yi a gidan aurenta, ko da kuwa a halin yanzu an yi nazarin kamar ba ta da wannan siffar. Idan kuma ya kasance an nazarci cewa wacce ake son a nema da aure ba ta da wadannan dabi’un, kuma ba ta da saukin hali, in dai tana da rikon addini, to mutum sai ya binciki kansa, ya yi nazarin wannan siffa ta iya nuna soyayya a gare shi, in har ya ga zai iya rayuwar aure ba lallai sai da ita ba, sai ya ci gaba da hidimomin neman aurensa.
3. Zabar Mace Mai Haihuwa: Kamar yadda ya gabata a sama, cewa Annabi SAW ya yi umarnin a auri mace mai haihuwa, musamman don al’umma ta yawaita. Kuma haihuwa tana daga cikin manyan abubuwan da ake kulla aure dominsu, domin samun zuri’a na daga cikin dadadan abubuwan rayuwar duniya. Don haka mutum zai yi dubi zuwa ga zuri’ar gidansu macen da yake da niyyar aure, in sun kasance masu haihuwa ne, to ana kyautata zaton ita ma mai haihuwa ce. Sannan in an samu kyakkyawar fahimta, ana iya zuwa a yi binciken kimiyya a asibiti don kore yiwuwar rashin haihuwa tsakanin duka mace da namijin.
2. Zaben macen da ta dace da bukatar maniyyaci: Kamar yadda ya zo a bayanan da suka gabata, dole mutum ya yi nazarin kansa da yanayin bukatuwar ransa lokacin da yake da niyyar aure, domin hakan zai taimaka masa ya zabo wacce ta dace da bukatunsa ta kowace fuska. Maniyyacin aure zai zabi irin matar da yake ganin ta dace da shi ta bangarori uku:
1. Siffa da kirar jiki: Sai maniyyaci ya zabo macen da ya fahimci ta fi kayatar da shi ta fannin kirar jiki da sauran siffofi na halitta: watau fara, baka ko wankan tarwada; doguwa, gajera ko tsaka-tsaki; mai kiba, siririya ko madaidaiciya; dirarriya ko marar diri; da sauran abubuwa makamanta.
2. dabia/Halayya: Mutum yana son mai shiru-shiru, ko ya fi son mai yawan surutu; mai hakuri da kau da kai yake so ko masifaffiya; mai yanga da jan aji yake so ko mai saukin kai da haba-haba da jama’a; mai wayewa yake so ko wacce ba ta waye ba? Da sauran siffofin dabi’a makamanta wadannan.
3. Matsayi/Asali: Sannan maniyyaci ya yi nazarin ko yana da bukatar wani asali ko wani matsayi tare da matar da yake son ya aura ko kuwa wannan bai dame shi ba? Misali, in zuciyarsa ta karkata ga shi sai ’yar gidan manya; ko ’yar sarauta, ko ’yar masu kudi, ko ’yar malamai, ko sai mai ilimi mai zurfi, ko sai mai aiki, ko shi bazawara yake so, ko ’yar wata kabila daban da kabilarsa yake so, da sauran abubuwa makamanta. Domin in ya auri wacce ba ta tare da wannan siffa da yake so, to haka zai rayu da ita yana jin akwai wani rauni a tare da ita.
Sai maniyyacin aure ya zauna ya siffanta abubuwan da yake son a ce matar da zai aura ta mallake su; don yin nazarinsu lokacin da ya ga wadda yake so ya fara neman aure. Rashin zabar macen da ta dace da bukatar maniyyacin aure na iya zama dalilin samun matsaloli bayan aure.
Yayin bai wa wannan bangare muhimmanci sama da bangaren addini kuma, sai ya zama dalilin samun matsaloli cikin rayuwar aure. Da yawa in muka lura aure-aure a wannan zamani an fi bai wa dacewar mace da bukatuwar rai sama da dacewa ta fuskar addini; wanda hakan ke haifar da yawan mace-macen aure; domin ita bukatar rai kullum canzawa take yi, shi kuwa addini yana nan din-din-din.
4. Zaben Macen Da ta Dace Da Ahlinsa: Maniyyacin aure ya sani, macen da ya aura ba shi kadai zai yi mu’amala da ita ba, har iyayensa da ’yan uwansa ma za su yi mu’amula da zumunci da ita; don haka sai ya kula wajen zaben wacce za ta yi daidai da al’adar gidansu a yadda ya san ta, wacce kuma ta dace da matsayi ko asalin zuri’arsu a cikin al’umma. Duk macen da aka tabbatar aurenta zai iya zama matsala ga iyaye, ’yan uwa da dangi; to ya fi kyau a hakura a sake neman wata mafi dacewa.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.