✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Neman Matar Aure 2

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban neman matar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa.

Ladabi Na 5: Zabar Macen Da ta Dace: Aure wani abu ne da ake kulla shi don samun natsuwa, farin ciki da annashuwar zuciya ga ma’aurata da kuma samar da kyakkyawar zuri’a wacce za ta samar da ingantacciyar al’umma. Kamar yadda Allah SWT Ya fada cikin littafinSa mai tsarki:

“Kuma akwai daga cikin AyoyinSa Ya halitta muku matan aure daga kawunanku, domin ku natsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahma a tsakaninku. Lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani. Rum 21.
Don samun dacewa da irin wannan natsuwar zuciyar, dole sai ma’aurata sun zabi miji ko matar da tafi dacewa da su ta kowane fannin rayuwar duniya. Haka kuma Manzon Allah SAW Ya yi Umarni ga mai niyyar aure da cewa ya sa kulawa sosai wajen zabar mace domin irinsa (zuri’arsa), kuma ya ce mutum ya auri mafi dacewa (daga mata) kuma ya aurar da ’ya’yansa ga mafi dacewa.
Maniyyacin aure zai dubi dacewar matar da zai aura ta fuskoki uku: ta fuskar addini, ta fuskar yanayin bukatarsa da kuma dacewarta da yanayin zamantakewar danginsa. Ga bayaninsu daya bayan daya:
Dacewa Ta Fuskar Addini: Idan muka bibiyi koyarwar addinin Musulunci za mu ga cewa siffofi uku ne suka dace maniyyacin aure ya yi la’akari da su lokacin zabar matar da zai aura- na farkonsu, kuma mafi muhimmancinsu shi ne riko da addini, sai iya mu’amalar soyayyar aure, na ukunsu shi ne mace ta kasance mai haihuwa ce.
1. Riko da Addini: A cikin wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah SAW ya yi kyakkyawan bayani kan irin macen da ta dace a nema da aure, inda ya ce:
“Ana auren mace saboda abubuwa guda hudu: arzikinta, asalinta (dangantakarta), kyawunta ko addininta. Na hore ku da auren mai addini, in ba haka ba kuwa za ku tabe.”
A wani kaulin kuma ya ce “Na hori ku auri mai addini za ku samu natsuwa…”
Daga wannan umarni na Manzon Allah SAW, za mu fahimci cewa, mace mai riko da addini, ita kadai ce macen da ta halatta a nema da aure, ita kadai kuma ya halatta a aura! Musamman in muka yi la’akari da kalaman karshe na cikin wannan Hadisi wanda gargadi ne mai karfi da hadarin da ke tattare da auren mace marar riko da addini, sannan a wani Hadisi daban Annabi SAW Ya siffanta salihar mace da cewa ita ce, mafi kyawun abin da dan Adam zai mallaka a duniya. Don haka duk wanda ya nemi auren mace da ba ta riko da addini, to ya juya baya ne ga wannan umarni na Annabinmu SAW. Kuma wannan ya nuna shi ma yana da nakasu wajen riko da addini, ba ya kishin addini, kuma ba ya kwadayin a haifa masa zuri’a masu riko da addini. Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada cikin littafinSa mai tsarki:
“Miyagun mata domin miyagun maza suke,sannan miyagun maza domin miyagun mata suke. Kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke, kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke…” -Suratun Nur, Aya ta 26.
Wani abu kuma mai kyau game da wannan ingantaccen Hadisi shi ne, da a ce dukkan Musulmi za su yi aiki da shi, su wanzar da shi cikin rayuwarsu, to da ya gyara da kuma tsarkake al’umma gaba daya; domin in duk namijin da ya tashi aure zai nemi mai riko da addini ya aura, to da kowace mace ta dage da rikon addininta don samun mijin aure. Wannan shi zai sa ’ya’yan da za a rika haifa cikin al’umma su zama nagartattu masu tarbiyya domin iyayensu sun kasance masu riko da addini.
Ya ake gane mace mai riko da addini?
Mu sani, imani a zuciya yake, ba a iya gane mace mai addini daga ganin ido kawai, ko daga yanayin shigarta ko mu’amularta; domin da yawan mutane a wannan zamani suna nuna fuskokin riko da addini, amma idan za a yi kyakkyawan nazari, sai a tarar yanayin dabi’unsu sun yi nesa da koyarwar addinin.
Don haka ba wai da ganin mace mai sa hijabi, yawan zuwa islamiyya, kame kai ko yawan jin kunya ne sai a ce an samu mai riko da addini ba, dole sai an zurfafa bincike an tabbatar cewa riko da addini ba a zahiri ba ne kadai, a’a, har a badini cikin zuciya, abin haka yake.
Za a yi irin wannan zurfaffen binciken ne ta hanyar tambayar wadanda suka santa, suka zauna da ita kuma suka yi mu’amula da ita na tsawon lokaci, kamar kawayenta, makwabtan gidansu, malaman makarantarsu na da can da na yanzu, ’yan ajinsu a makaranta, ‘Yan uwanta na bangaren uwa da na uba, da sauran duk wanda aka ga yana da muhimmanci a rayuwarta da zai iya bayar da wani bangare na yanayin halayyarta, dabi’unta da kuma mu’amularta.
Sannan wajen yin irin wannan bincike dole sai an sa kulawa da taka tsan-tsan, saboda yanayin gurbacewar zamani, da yawan mutane zuciyoyinsu dauda ta yi yawa, wasu za a iya tambayarsu su ki fadar gaskiyar da suka sani game da yarinyar da ake bincika, wasu na yin haka da nufin wai kada su fadi asalin halayenta marasa kyau su hana mata samun mijin aure, wasu kuma suna yin haka da nufin hassada da jin kyashi kada su fadi kyawawan halinta auren ya yiwu, don haka sai su fadi halayen da take da rauni kadai, su ki fadar halayen kirkinta, wasu ma sukan zauna su shirya karairayi na muzantawa don dai su hana yiwuwar auren. Don haka maniyyacin aure sai ya sa lura da kiyayewa da irin wadannan mutane yayin da yake bincike, duk maganar da ya ji mai kyau ko marasa kyau kada ya dauke ta a haka har sai ya kara bincikawa ta wata kafar daban ya tabbatar da ingancinsu kafin yin aiki da su.