Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shine zaben macen da ta dace; da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin
Yadda ake gane masoyiyar mace: Duk mace mai addini za a same ta da kamun kai da natsuwa, ba ta sakin fuska ga duk namijin da bai halatta a gare ta ba; don haka ba a iya gane yanayin dabi’arta farat daya dole sai an yi kyakkyawan nazari yadda take zamantakewa da kawayenta da sauran mutanen da ya halatta ta saki jiki da su kamar kannenta da mata ’yan uwa ko makwabta. In ta kasance mai saukin hali gare su, mai yi musu ayyukan sadaukarwa, mai kokarin faranta musu rai a kai-a-kai, mai yawan yin wasa da dariya da su, mai saurin hucewa da yafewa yayin da wani abu ya shiga tsakaninsu; to wannan tana da siffofin masoyiyar mace. In kuma aka yi rashin sa’a ba ta da wadannan siffofi, to sai a yi nazarin in tana da saukin hali da kuma saurin fahimta, ta yadda bayan aure mijinta in ya mu’amulance ta da wasannin soyayya, saukin halinta zai sa nan da nan ita ma ta koya kila ma har ta fi shi iyawa. Sannan za a iya yin dubi ga mahifiyar wadda ake neman auren, in aka tarar ta iya zamantakewar aure da mijinta, to ana kyautata zaton ’yarta ma haka za ta yi a gidan aurenta koda kuwa a halin yanzu an yi nazarin kamar ba ta da wannan siffar. In kuma ya kasance an nazarci cewa wacce ake son a nema da aure ba ta da dabi’un masoyiyar mace, kuma ba ta da saukin hali, in dai tana da rikon addini, to mutum sai ya binciki kansa, ya yi nazarin wannan siffa ta iya nuna soyayya a gare shi, in har ya ga zai iya rayuwar aure ba lallai sai da ita ba sai ya zarce ya ci gaba da hidimomin neman aurensa.
- Zabar mace mai haihuwa: Kamar yadda ya gabata a sama, cewa Annabi (SAW) ya yi umarnin a auri mace mai haihuwa, musamman don al’umma ta cika ta yi yawa. Kuma haihuwa tana daga cikin manyan abubuwan da ake kulla aure dominsu, domin samun zuriya yana daga cikin dadadan abubuwan rayuwar duniya. Don haka mutum zai yi dubi zuwa ga zuriyar gidan su macen da yake da niyyar aure in sun kasance masu haihuwa ne, to ana kyautata zaton ita ma mai haihuwa ce. Sannan in an samu kyakkyawar fahimta, ana iya zuwa a yi binciken kimiyya a asibiti don kore yiwuwar rashin haihuwa a tsakanin mace da miji.
- Zaben mace da ta dace da bukatar maniyyaci: Kamar yadda ya zo a bayanan da suka gabata, dole mutum ya yi nazarin kansa da yanayin bukatuwar ransa lokacin da yake da niyyar aure, domin hakan zai taimaka masa ya zabo wadda ta dace da bukatunsa ta kowace fuska. Maniyyacin aure zai zabi irin matar da yake ganin ta dace da shi ta bangarori uku:
- Siffa da kirar jiki: Sai maniyyaci ya zabo macen da ya fahimci ta fi kayatar da shi ta fannin kirar jiki da sauran siffofi na halitta: wato fara, baka ko wankan tarwada; doguwa, gajera ko tsaka-tsaki; mai kiba, siririya ko madaidaiciya; dirarriya ko maras diri da sauran abubuwa makamanta.
- Dabi’a/Halayya: Mutum ya san mai shiru-shiru ya fi so ko mai yawan surutu; mai hakuri da kau da kai yake so ko masifaffiya; mai yanga da jan aji yake so ko mai saukin kai da haba-haba da jama’a; mai wayewa yake so ko wadda ba ta waye ba? Da sauran siffofin dabi’a makamanta wadannan.
- Matsayi/Asali: Sannan maniyyaci ya yi nazarin ko yana da bukatar wani asali ko wani matsayi tare da matar da yake son ya aura ko kuwa wannan bai dame shi ba? Misali, in zuciyarsa ta karkata ga sai ’yar gidan manya; ko ’yar sarauta, ko ’yar masu kudi, ko ’yar malamai, ko sai mai ilimi mai zurfi, ko sai mai aiki, ko shi bazawara yake so, ko ’yar wata kabila daban da kabilarsa yake so, da sauran abubuwa makamanta. Domin in ya auri wadda ba ta tare da wannan siffa da yake so, to haka zai rayu da ita yana jin akwai wani rauni a tare da ita.
Sai maniyyacin aure ya zauna ya siffanta abubuwan da yake so a ce matar da zai aura ta mallake su; don yin nazarinsu lokacin da ya ga wadda yake so ya fara neman aure. Rashin zabar macen da ta dace da bukatar maniyyacin aure na iya zama dalilin samun matsaloli bayan aure. Yayin da bai wa wannan bangare muhimmanci sama da bangaren addini kuma sai ya zama dalilin samun matsaloli cikin rayuwar aure. Da yawa in muka lura aurarraki a wannan zamani an fi bai wa dacewar mace da bukatuwar rai sama da dacewa ta fuskar addini; wanda hakan ke haifar da yawan mace-macen aure; domin ita bukatar rai kullum canjawa take yi shi kuwa addini yana nan dindindin ba ya canjawa.
- Zaben macen da ta dace da ahlinsa: Maniyyacin aure ya sani, macen da ya aura ba shi kadai zai yi mu’amala da ita ba, har iyayensa da ’yan uwansa ma za su yi mu’amula da zumunci da ita; don haka sai ya sa kula wajen zaben wacce za ta yi daidai da al’adar gidansu a yadda ya santa, wacce kuma ta dace da matsayi ko asalin zuriyarsu a cikin al’umma. Duk macen da aka tabbatar aurenta zai iya zama matsala ga iyaye, ’yan uwa da dangi; to ya fi kyau a hakura a sake neman wata mafi dacewa.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.