Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya kamar kullum. A wannan mako mun kawo muku ‘labarin Zaki da Bawa.’ Labarin ya kunshi yadda manyan gobe za su zama masu taimako a inda ake bukatar taimakonsu. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Zaki da Bawa
An yi wani azzalumin sarki a wani kauye. Yana kuntata wa bayinsa a kullum ga shi kuma ba ya ba su abinci yadda ya kamata. Abin ya ishi bayin kuma ba su san yadda za su yi ba.
Wata rana sai daya daga cikinsu ya gudo zuwa daji. Ya shiga cikin kogon zaki. Yana cikin hutawa ke nan sai ya ji wata kara kamar ta zaki. Waigawar da ya yi sai ya ga katon zaki jina-jina wani karfe ya kama shi a kafa.
Nan take ya je ya taimaka wa zakin sai suka zama abokai.
Da sarki bai ga bawansa ba sai ya sa aka shiga nemansa har aka kama shi. Sarki ya ce zai yi masa mummunan horo saboda ya zame wa sauran bayin darasi. Sarki ya sa aka taro mutanen kauyensa, aka sanya wannan bawan a wani fili zagaye da itatuwa, sai aka sako masa zaki.
Mutanen kauyen suka zuba ido don su ga abin da zai faru. Sai suka ga zaki ya fara lashe bawan sarki. Ashe zakin da bawan ya taimakawa ne sarki ya sa ya kashe bawan. Abin ya ba wa sarkin mamaki. Sai ya hakura da hukuncin kisan da ya yanke wa bawansa. A haka aka sake shi.
Da fatan Manyan Gobe za su zama masu taimako kuma su dauki darasi a wannan labari.