Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon za mu kawo muku karshen labarin wasan buya a rayuwar aure da muke kawo muku makonni biyar da suka gabata. Muna fata za ku rika amfani da darussan da labarin yake koyarwa.
Daga Al-Bint’s Diary
Fassara: Bashir Musa Liman
Tahir ya ci gaba da ba Bint labari, inda ita kuma ta zuba masa idanu tana saurare:
“Na kuma yi wa dan uwansa kaca-kaca a kan abin da ya yi. Kai daga farko ma ban yarda cewa auren da aka daura ya dauro ba, hakan ya sa na ce masa anya ’ya’yan ma kuwa ba shegu ba ne, hakan ya sa ya kira dan uwansa Isa don ya ba da shaida, sannan ya ce masa ya zo da shaidar da za ta gamsar da su an yi aure na gaskiya, na ga hotunan bikin, hakan ne ya tabbatar mini da auren, na ga hotunan limamin da ya daura auren, da ’yan uwan Wasila da sauransu.
“Daga nan ne ya sa na je bikon Hajara wajen iyayenta. Na sha wahala kafin na gamsar da su ba mu san yana da wannan matar ba. Daga nan suka ce ba za takura wa hajara ba, zabi ya rage nata, idan ta ga dama ta koma, idan ta ga dama ta kashe auren. Bayan na same ta ne ta ce mini sai ta yi tunani domin ba ta tsammanin Usman zai yi mata haka ba. Ta ce mini ya kamata a ba ta kamar wata daya, domin a yanzu ba ta da natsuwar da za ta iya yanke wani hukunci.
“Ta ce mini duk bayan kwana uku ko hudu zai ce mata an tura shi aiki wani gari, ashe a wadannan ranakun yake zuwa wurin matarsa ta farko, yanzu daga wurin Hajara nake, ba zan fada masa hukuncin da ta yanke ba har sai ya sake zuwa wurina a bukace.” Tahir ya kammala ba ni labari. Bayan na kalle shi.
“Duk da haka Hajara za ta iya sanar da ’ya’yanta cewa mahaifinsu ya yi auren sirri. Amma ga bangaren Zahra’u yaya za ta sanar wa ’ya’yanta ta yadda aka samu dan uwansu?” Na tambaye shi ba tare da na yi tsammanin zai ba ni amsa ba.
Bayan Tahir ya yi murmushi ya ce: “Tun da an ba ta Naira miliyan biyar a matsayin toshiyar baki, ai za ta samu wata hanyar da za ta ba su labarin dan uwansu. Don haka kada ki damu kanki Bint, amma idan an ba ki wani kamisho ne kuma wannan za ki iya bata lokaci wajen tunanin yadda za ta ba su labarin. Yanzu kam ya kamata in fita kafin ki sa in makara.”
Na kalle shi bayan ya mike tsaye, kamar zan ce wani abu sai na yi murmushi, tun da na gane ya fadi haka ne don ya zolaye ni. Har ya fita bai daina murmushi ba, ni kuma ban ce masa wani abu ba. A karshe na ce: “Wannan shi ne labarin buya a rayuwar aure.”
Mun kammala.
Iyayen Giji: Ina fata kun karu da darussan da ke cikin wannan labarin, sannan kun fahimci fadin gaskiya a cikin rayuwar aure na daya daga cikin sinadaran da za su sanya aure ya yi karko, gara ka fada wa mutum gaskiya ya ji haushi, maimakon ka fada wa mutum karya ya ji dadi daga baya ya gane karya ka fada masa.