Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban labarin wasan buya a rayuwar aure da muke kawo muku. Muna fata za ku ci gaba da bin labarin sau da kafa don fa’idantuwa da darussan da yake koyarwa. A sha karatu lafiya:
Daga Al-Bint Diary
Fassara: Bashir Musa Liman
‘Eh, wannan ba matsala ba ce.” Ya ce da ita kai tsaye ba tare da yana kallonta ba. Ta dawo cikin dakin, sannan ta samu wuri ta zauna. Bayan ya yi ta ’yan maza sai ya fara magana:
“Daga farko dai ina kara gode miki bisa ga yadda kika nuna karimci jiya da daddare, mahaifiyarsa abokiyar aikina ce, shekara shida da ta gabata aka tura mu wani kwas a wani gari, bayan an tashi daga kwas din na rage mata hanya, na kai ta gidanta, a kan hanya take sanar da ni ita kadai take zama, kasancewar iyayenta suna kauyensu, kamar wasa sai na rika kai mata ziyara, kin san zuciya ba ta da kashi, kafin ka ce wani abu sai aka samu cikin yaron nan. Daga nan ta rika matsa mini a kan na aure ta, amma ba ni da wannan ra’ayi, mahaifiyarsa tana da wuyar sha’ani, ta cika korafi, ga ta da kananan maganganu, sannan ba ta da hakuri, daga baya ne na fahimci hakan. Bayan ta je hutun haihuwa sai ta yi ritaya, daga nan na ci gaba da daukar nauyin yaron, yanzu tana aiki a wani wuri, amma kullum tana cikin yi mini barazanar in dauki dana idan ba zan aure ta ba, ko jiya ma barazanar ta ci gaba da yi mini ke nan.
“Ina shiga gidanta jiya sai turo mini yaron, sannan ta miko mini akwatinsa, ta ce ba ta son wani abu ya ci gaba da kasancewa a tsakaninmu. Na dauke shi, sannan na ci gaba da yawo da shi a cikin gari ba tare da na san me zan yi ba, daga karshe na yanke shawara in kawo shi gida idan ya so ki yanka namana ki cinye, amma na rika fatan ki bar shi ya kwana zuwa yau. Ba ki ji dadin da na ji a kan abin da kika yi jiya ba. Na gode miki matuka.” Ya ja dogon numfashi bayan ya kammala jawabinsa, daga nan ya ci gaba da kallonta.
“Yanzu kana nufin zai ci gaba da zama da mu ke nan?” Ta tambaye shi.
“Haka nake fata, amma idan ba ki amince ba sai in kai shi wurin mahaifiyata.” Ya fada mata kai tsaye, ba tare da ya kalle ta ba.
“Na tabbata yaran nan ba za su damu ba, amma ta yaya za mu yi musu bayani?” Zahra’u ta tambaye shi.
“Ke ce za ki taimaka mini da haka Zahra’u, ki yi musu bayanin yadda za su fahimta, na san yadda zan tunkari mahaifiyata da kuma sauran ’yan uwana, na san wannan lokaci zai zama mafi tsanani a gare ni, kuma jarrabawa ce a gare ni, amma da Yardar Allah zan ci wannan jarrabawar. Na kuma yi alkawarin ba zan sake jefa kaina a cikin mummunan hali irin wannan ba.” Ya fada mata, a lokaci guda ya yi mata murmushin karfin gwiwa. Hakan ya sa na ce “A yanzu dai Zahra’u ta mallaki Naira miliyan 5, amma ta shiga tsaka-mai-wuya wajen don ta yi wa ‘ya’yanta bayani.
“Yanzu kina nufin ki ce kowane da namiji kamar mijin Zahra’u yake ke nan?” Tahir ya tambaye ni.
“Ai mutum abin tsoro ne…” Bayan na sanya hannuna a cikin nasa sai na ce: “Wannan shi ne wasan buya a cikin rayuwar aure.”
“Hakan na nufin dai cewa ke ma kin dauki kowane namiji kamar mijinta yake ke nan?” Tahir ya sake tambaya ta.
“Kamar yadda na fada maka, dan Adam abin tsoro ne.” Bayan na ci gaba da wasa da hannunsa.
Bayan ya cire hannunsa daga cikin nawa, sai ya fuskance ni, na ci gaba da kallonsa, domin na san zai fada mini magana mai muhimmanci.
Za mu ci gaba in sha Allahu.