✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin wasan buya a rayuwar aure

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon na kawo muku labarin wasan buya a rayuwar aure. Ina fata za ku…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon na kawo muku labarin wasan buya a rayuwar aure. Ina fata za ku bi labarin bi-da-bi don ku karu da darussan da ke cikinsa.

Daga Kundin Al-Bint
Fassara: Bashir Musa Liman

“Za ki iya ba ni abincin karyawata yanzu?” Tahir ya tambaye ni bayan ’ya’yanmu sun fita don zuwa makaranta.
“Me zai hana, dalilin da ban kawo maka ba shi ne, na ga ba ka saba karin kumallo yanzu ba ne.” Na ba shi amsa a lokacin da na mike don in nufi kicin.
“Ina da wata ganawa ta musamman ne, wanda za ta iya kai ni karfe sha biyu na rana, idan ban ci abinci yanzu ba zan iya azumin dole ke nan.” Ya yi mata bayanin dalilin da ya sa ya bukaci abinci.
“Babu matsala, bari in hada maka abinci cikin gaggawa in sha Allah.” Na ce da shi bayan na kusa isa kofar shiga kicin din.
Bayan minti 40 na kammala shirya masa abinci a kan teburin cin abinci. Ya ci gaba da cin abincin ina kallonsa, amma ina ta sake-sake a zuciyata, can na ji ba zan iya danne tambayar da nake so in yi masa ba. Bayan na kalle shi, sai na tambaye shi:
“Tahir, idan har ka haihu da wata mata a waje za ka iya tunkara ta ido-da-ido ka fada mini?”  Saura kadan abincin da ke cikin cokalin da ke rike a hannunsa ya zube, cikin kaduwa ya ba ni amsa:
“Me zai kai ni ga haihuwa kuma a waje? Ya tambaye ni.
“Ba wai ina maka fatan ka haihu a waje ba ne, amma idan kaddara ta kaddaro haka saboda sharrin shaidan…” Nake kokarin fahimtar da shi, amma ya katse ni.
“Ban taba tsammanin za ki yi mini mummunan fata irin wannan ba. Na yi kokari wajen bin abin da kur’ani ya ce: “Kada ku kusanci zina’, don haka ban taba kusantar zina ba, ballantana na aikata ta, da yaya zan samu dan shege ke nan?” Ya ba ni amsa cikin bacin rai.
“Na yi wannan tambayar ce kawai don in ji idan kai ne yaya za ka iya sanar da ni?” Na ce da shi bayan na yi murmushin kwantar masa da hankali.
“Hakan ba zai taba faruwa ba in sha Allahu, idan har kuma kin yi wannan tambayar don ki daga mini hankali har in kasa cin abincin ne, to hakarki ta cim ma ruwa, yanzu ba na jin yunwa.” Ya ce da ni bayan ya kalle ni, sannan ya ture farantin abincin da ke gabansa.
“Ka yi hakuri, na yi maka wannan tambayar ce saboda abin da ya faru da kanwata Zahra’u. Na fada maka ne saboda al’amarin ya addabi zuciyata, ya hana ni rawar gaban-hantsi, ka ci abincinka kawai saboda ka ce za ka yi ganawa ta musamman. Ba zan sake damunka ba.” Na ba shi hakuri.
“Ok, amma na san akwai wani abu mai muhimmancin da kike son fada mini, me kuma ya faru da Zahra’u?” Ya tambaye ni bayan ya ci gaba da cin abincin. “Tun da nake ban taba jin wani abu na bakin ciki da ya faru da wata ’ya mace kamar abin da ya faru ga Zahra’u kwanaki uku da suka gabata ba. Shekaranjiya ta zo wurina cikin kuka, abin da ta sanar da ni ya daga mini hankali. Na yi mamakin irin karfin halin da take da shi. Mijinta yana da dabi’ar barin gida duk lokacin da ya ci abincin dare tsawon shekara biyu ke nan kowace rana. Zai yi wanka, ya sanya tufafi masu kyawu da kuma tsada, ya fesa turare mai kamshi, sannan ya ce ya tafi hira wurin abokansa. Zahra’u ba ta taba tambayarsa ko yi masa korafi a kan abin da yake yi ba, kwanaki biyu da suka wuce, ya yi wanka ya sanya tufafi masu tsada, sai dai a wannan rana ya dade fiye da ranakun da yake fita a tsawon shekara biyu. Ta ce mini baya wuce karfe 10:30 na dare a waje ba tare da ya dawo gida ba. Yawancin lokutan takan yi kamar ta kira lambarsa sai ta fasa, saboda ba ta san me zai fada mata ba…”
Za mu ci gaba in sha Allah.