“Na yi iya bakin kokarina wajen ganin na koyi girki mai dandano da gamsarwa, amma hakan ya gagara. Hankalina ya tashi, domin duk lokacin da na yi girki Auwal ba ya iya ci, saboda ba ya yin dadi. Wannan ta zama babbar matsala a tsakaninmu. Tunda na kasa gamsar da shi a wurin girki, sai ya daina cin abincin da na girka. Yadda na girka na zuba masa, haka zan kwashe kwanukan ba tare da ya yi ko loma daya ba.
“Wannan ya sanya na kasa natsuwa; na kuma kasa jurewa, sai na sanar da mahaifiyata hakikanin halin da nake ciki. A nan ta rika shiga tana fita. Ta ce wa ya ce na je gidan Auwal ne don na zama baiwa ce. Haka ta rika shiga tana fita. Ana yin aure a kara kyau da haske, a kuma samu kwanciyar hankali, amma gaba daya na rame. Sai dai a yi wacce za a yi, idan ba za a dauko mai girki ba.
“Wasa-wasa karamar magana ta zama babba, domin al’amarin ya haifar da zazzafar muhawara tsakaninmu. Mahaifiyarmu ta tsaya kai da fata sai dai a dauko mini mai girki, Auwal kuma ya jajirce sai dai na rika girka masa abinci, ba shi da wani buri face ya rika cin abincin da matarsa ta girka. Na yi bakin kokarina don na iya girkin da zai gamsar da shi, amma al’amarin ya gagara.
“Wata rana ya ce na shirya masa hadadden girki domin abokansa da suka yi jami’a tare sun kawo masa ziyara, don haka zai zo da su su ci abinci. A nan fa hankalina ya tashi domin ba na so na yi abin da zai bata masa rai, ina da shakkar ba lallai ne abinci da zan girka ya gamsar da su ba. Haka dai na yi bakin kokarina. A karshe dai abinci bai samu tagomashin dandano mai dadi daga bakin Auwal da kuma abokansa ba, domin kashi daya bisa uku na abincin suka ci. Tun daga ranar ya canza mini. Ba ya damuwa da duk wani abu da ya shafe ni, idan ya dawo zai yi abin da ya dame shi ne kawai. Na kasa daurewa domin ina sonsa tsakani da Allah, kuma ina bakin kokarina don ganin na faranta masa. Na ba shi hakuri, amma sai ya fara fada wai bai taba ganin dakikiya irina ba, wata da watanni ana abu daya, na kasa iya girki. Duk da kalamansa sun yi mini zafi, sai na yi hakuri, domin na san abin da hakuri bai bayar ba rashinsa ma ba zai bayar ba.
Labarin Raliya a gidan aure (4)
“Na yi iya bakin kokarina wajen ganin na koyi girki mai dandano da gamsarwa, amma hakan ya gagara. Hankalina ya tashi, domin duk lokacin da…