A daren rana,r ya sanar da ni girkina yake so, ba wai na wata ba. Akwai wuraren cin abinci da yawa a gari, amma nawa yake so, don haka ba ya so, daga yau, na rika kiran wata don za ta dafa abincin da shi kadai zai ci, wanda shi ba giwa ba ne ballantana a ce sai an yi taron dangi kafin a dafa abincin da zai ci.” Ta yi shiru, bayan ta daidaita numfashinta sai ta ci gaba.
“Na sassauta muryata, sannan na lalubo murya mafi taushi da laushi kafin na fara ba shi hakuri: ‘Kada ka damu masoyina, ba ni da wani buri face na faranta maka, zan dage wurin ganin ka samu dukkan abin da kake so’. Ya yi murmushin karfin hali. Na bi shi da kallo, a lokaci guda na sake sassauta muryata, domin duk da murmushin da ya yi, na gane zuciyarsa ba ta sauko ba. Haka yake, yana da saurin fushi. Masu hikimar zance sun ce, idan ka san halin mutum, ka sha maganin zaman da shi. Hakan ya sanya na ci gaba da yi masa dadadan kalamai masu dauke da sinadaran hakuri da kuma kwantar da zuciya. Daga karshe ya yi murmushin jin dadi. Daga nan muka ci gaba da hira, har a karshe muka yi barci cikin kwanciyar hankali.” Bayan ta sake yin shiru ne, sai na tambaye ta me kuma ya faru a gaba?
“Washegari na nemi izinin zuwa gida don na gaishe da mahaifana. A nan muka rika bugawa a kan zai kai ni, ni kuma saboda akwai boyayyen dalilin da ya sa nake son zuwa gidan ni kadai, sai na rika zillewa, har Allah Ya tarfa wa garina nono, na yi dabarar da ya yarda na tafi ni kadai. Da yake na iya mota kuma ina da mota, sai muka yi sallama. Auwal ya tafi wurin aiki, ni kuma na ci gaba da shiri. Bayan na kammala ne na kama hanyar zuwa gida. Gani daya mahaifiyata ta yi mini, ta san akwai abin da yake damuna. Yanayinta ne ya sauya ta kuma ci gaba da yi mini wani irin kallo mai dauke da alamar tambaya. Ta kasa hakuri, bayan ta kira ni har na zo na zauna kusa da ita a kan wata doguwar kujera da ke falon gidanmu ne ta tambaye ni ‘’yar baba. me ya yi cacukwi da kwalar rayuwarki?’ Na yi shiru zuwa wani lokaci sannan na ce mata, ‘Auwal ne yake so na rika dafa masa abinci. Wai ba ya son cin girkin kowa, sai nawa’. Ta yi shiru, sannan ta ja dogon numfashi, domin tana da masaniyar a nan ne matar za ta kada mijin, ma’ana ta san ban iya girki ba. ‘Kada ki damu, za mu san yadda za mu yi’. Daga baya ne na nemi izinin mijina don a kawo wacce za ta koya mini girkin. Na yi sa’a ya amince.
Labarin Raliya a gidan aure (3)
A daren rana,r ya sanar da ni girkina yake so, ba wai na wata ba. Akwai wuraren cin abinci da yawa a gari, amma nawa…