Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon na kawo muku labarin wata baiwar Allah ce da rashin iya girki ya haifar mata da matsala a rayuwar aure, wanda hakan ya sa take so ta yi amfani da wannan filin don ta bayar da labarinta, don ya zama darasi ga sababbin da kuma tsofaffin ma’aurata mata.
Na fito daga wani shago bayan na sayi kayan shayi ke nan, sai wayata ta fara kadawa. Na ciro wayar daga aljihuna, sannan na kai kallona don tantance wanda yake kirana. A nan ne na ga bakuwar lamba, hakan bai ba ni mamaki ba, domin akalla kowace rana nakan amsa kiran bakin lambobi fiye da ashirin. Zan dauka ke nan sai wata mota ta zo wucewa ta kusa da ni, karar injin motar ya sa na yi jinkiri amsa kiran. Bayan motar ta wuce sai na amsa kiran ta hanyar yin sallama. Bayan ta amsa sallamar tawa ne, sai ta fara gaishe ni cikin murya mai cike da ladabi da kuma girmamawa. Na rika amsa mata zuciyata cike da tunani da me ta zo.
“Sunana Raliya (ba sunan gaskiya ba). Akwai magana mai muhimmanci da nake so mu yi.” Ta ce cikin muryar girmamawa. “Don Allah ki kira ni nan da kamar minti goma a lokacin na koma gida, domin yanzu haka ina waje.” Na nemi uzurinta.
Bayan ta ce babu damuwa sai ta kashe wayar. Tambayoyi masu yawa sun ziyarci zuciya da kwakwalwata, haka na ci gaba da tafiya har na isa gida. Minti goma na cika na ga kiranta ya shigo. Cikin zumudi na amsa kiran, sannan na daidaita numfashina ta hanyar natsuwa da tattara hankalina gare ta don jin me ke tafe da ita.
“Kamar yadda na fada maka sunana Raliya (ba sunan gaskiya ba). Mun yi auren soyayya; ni da mijina. Kafin aurenmu mun yi soyayya abar kwatance, ta zama abar sha’awa a wurin mutane. Sun ce soyayyarmu kamar ta masoya Romeo da Juliet take. Farin cikina nasa ne kamar yadda bakin cikinsa yake nawa. Idan muna tare sai duniyarmu ta dawo sabuwa. Idan muna tare mukan samu natsuwa, idan mun rabu hankalinmu ba ya dawo wa jikinmu sai mun sake ganin juna.” Ta yi shiru zuwa wani lokaci, a nan sautin numfashinta ya ci gaba da amayowa, wanda hakan ya ba ni damar kallon labulen tagar dakina. Bayan na gyara zama sai na kara tattara hankalina gare ta, domin na kagu na ji wainar da za a toya a labarin. Bayan ta tambaye ko ina jin ta na amsa ne, sannan ta ci gaba.
“Haka muka ci gaba da soyayya har ranar aurenmu ta zo. Aka yi biki na yada-kanin wani, hade da ruguntsumin da babu kama hannun yaro. Murna a wurinmu baki har kunne, burinmu ya cika.” Ta sake yin shiru. Daga nan na ji wayar tata ta fara wata irin kara. Zuwa wani lokaci sai ta ce mini ta gyara zama ne. Na ce mata babu komai.
“Haka muka ci gaba da soyayya kamar za mu hadiye kanmu. Mun fara samun matsala ne daga lokacin da na fara girki. Ba zan boye maka komai ba mahaifina attajiri ne. Mu uku ne a wurin mahaifanmu, kuma ni kadai ce mace. Na samu gatan da duk wanda ya samu irinsa zai yarda shi dan gata ne. Mahaifana ba sa son bacin raina. Wanki, wanke-wanke, girki da duk wani aiki ban iya ba.”
Za mu ci gaba.
Labarin Raliya a gidan aure
Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon na kawo muku labarin wata baiwar Allah ce da rashin iya girki ya…