Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Uba Sani, ya nesanta kansa da rahoton da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa ya kai kuduri gaban Majalisar Dattijai da ke neman sauya wa jihar Kaduna suna zuwa Zazzau.
Sanatan, wanda kuma shi ne dan takarar Gwamnan jihar ta Kaduna a karkashin tutar jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ya bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege.
- Jamus za ta sanya wa masu amfani da iskar gas sabon haraji
- Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 350 a Sakkwato
Haka kuma ya ce batun hada baki da ake cewa ya yi da Sanata Sulaiman Abdu Kwari mai wakiltar Kaduna ta Arewa don ganin kudurin ya tabbata shi ma shibcin gizo ne.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Sanatan ya bayyana takaicinsa kan lamarin tare da kira ga hukumomi da su nemo wadanda suka shirya zancen.
“Na yi mamakin wannan batu da na ji ya karade gari, kuma na san don a durkusar da takarata aka shirya hakan.
“Na san aikin ’yan adawa ne, amma menene alfanun yin hakan? Don kara rura wutar rashin tsaron da jihar ke ciki ko me?
“Sanata Uba Sani na da goyon bayan al’ummar jihar Kaduna, kuma wannan ba zai hana shi zama Gwamnan Kaduna ba karkashin jam’iyar APC a 2023,” inji shi.
Ya kuma ce duk wata bukatar kirkirar sabuwar jiha bisa dokar Najeriya, sai an tsefe ta a gaban kwamitin bitar kundin tsarin mulkin kasa tukunna.
Don haka a cewarsa, ya kamata jami’an tsaro su fara kokarin bankado marasa son zaman lafiyar da suka kirkiri zancen, don zamowa darasi ga masu tunanin aikata hakan.