✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Kaza da ‘yan uwanta

Barka da warhaka Manyan Gobe Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.A wannan makon na kawo muku labarin ‘Kaza da ‘yan uwanta’. Ina fata…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya.
A wannan makon na kawo muku labarin ‘Kaza da ‘yan uwanta’. Ina fata za ku bi labarin don ku tsinci darussan da yake koyarwa.

Labarin Kaza da ‘yan uwanta

A wani lokaci mai tsawo da ya wuce an yi lokacin da namun daji suka shiga halin kaka-ni-kayi da kuma hannu-baka-hannu-kwarya, sakamakon rashin abinci da ya addabe su, wani dadin a kan dadin kuma wai kunama a kan gymbo  shi ne, a shekarar an yi fari, sai abin ya zama goma-da-gomiya ga namun daji.
Sai da duk da wannan halin da aka shiga akwai wata kaza da take da buhun dawa uku a gidanta. A wata sanyin safiya, ‘yan uwan kaza suka je gidanta, bayan ta fito sun gaisa ne, sai daya ta yi amfani da bakin sauran kaji ta kuma ci musu albasa, wajen rokon kaza don ta taimaka musu da abin da za su ci. Ta ce: “Kamar yadda Allah Ya taimake ki shi ne muke so cikin abin da Ya hore miki din ki taimaka mana da dan abincin da za mu sanya a ciki, yau kwana biyu ke nan ba mu sanya komai a cikinmu ba, wadansu har sun fara mutuwa. Ki taimaka mana.”
Kaza ta yi musu kallon hadarin kaji, a lokaci guda ta kara kaikacewa sannan ta sheka musu kallon uku saura kwata. Cin daga murya da izza ta ce da su: “Lokacin da nake ta faman nema ina tarawa kuna ina? Na ga kun dauke ni wata sha-ka-ta-fi ce a lokaci guda kuka rika bushasha da kece raini, har ma da cin duniya da tsinke. Don haka tun kafin wankin hula ya kai ku dare, kuma tun kafin abin ya zama kamar yadda ruwa yake kare wa dan kada bai gama wanka ba, sai ku san na yi.”
Suka durkusa a gabanta sannan suka shiga yi mata magiya, amma ta ki saurararsu.
Ashe labarin kaza tana da buhun dawa tuni ya cika duniya kamar ruwan dare, kaji ba su dade da fita daga gidan kaza ba sai ga zaki manyan dawa ya shigo, dama masu magana sun ce idan ruwa ya ci ka, ko takobi aka miko maka kamawa za ka yi, don haka bala’in yunwar da ake yi ce, ta sanya zaki ya zo gidan kaza. Bai yi wata-wata ba ya shaida mata nufinsa, cikin tsoro jiki na kyarma ta janyo buhu daya da ta bashi, wanda hakan ya sanya saura buhu biyu ke nan.
Bayan zaki ya fita sai ga dila nan, cikin firgici kaza ta sake jawo buhun dawa daya ta ba ta.
Bayan dila ta fita ne sai ta yi tunani, a nan ta fahimci lallai duk wanda ya ki sharar masallaci to zai yi ta gidan giya. Daga nan ta je gidajen kaji ‘yan uwanta ta kuma ba su hakuri, sannan ta nemi da su je gidanta su ci abinci. Cikin murna da walwala suka ci abincin har suka koshi.