✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Binta marainiya

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon wakiliyarmu Hauwa Musa Aloko ta kawo muku…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon wakiliyarmu Hauwa Musa Aloko ta kawo muku wani labari mai kunshe da darussa masu yawa, muna fata za ku karanta labarin don fa’idantuwa da darussan da ke cikinsa.

Akwai wata rana na fita in je gidan abokiyata, sai na hadu da wata budurwa zaune a gefen hanya tana kuka. Kallo daya na yi mata na ji tausayinta ya ratsa zuciyata, hakan ya sanya na zauna kusa da ita bayan na karasa wurin da take. Na kara samun kaina cikin tsananin tausayinta bayan mun hada idanu, domin idanunta sun yi jajur kamar garwashin wuta, sun kuma kumbura kamar balan-balan.
Na yi mata murmushi don hankalinta ya kwanta, bayan na fuskance ta ne, ta kuma kalle ni sai na tambaye ta sunanta, kamar ba za ta amsa ba daga baya ta ce mini sunanta Binta.  Na tambaye ta me ya sa ta kuka, sai ta ce mini ta gaji da rayuwa, mutawa take so ta yi. Hankalina ya yi matukar tashi.”
“Me ya sa za kike so ki mutu?” Na ce da ita bayan na dafa kafadarta. Ta sanar da ni iyayen rikonta ne suke azabtar da ita, duk wani aikin gida ita take yi, ’ya’yansu na zuwa makaranta ita kuma kullum sai aikace-aikace gida, baya ga haka kullum ana cikin lakada mata duka, ga kuma gorin da ake yi mata.
Ta ce ta rasa iyayenta a hadarin mota, sannan iyayen rikonta suna ci gaba da gallaza mata azaba. Kullum ba ta da sukuni, takan ga mutane cikin walwala da jin dadi da kuma annushuwa, amma ita kullum cikin bakin ciki da azaba, ga shi an tsunduma ta a cikin kogin ukuba. Burinta ta mutu, domin hakan zai fi mata.
Hakan ya sanya na ce ta kwantar da hankalinta komai na rayuwa tamkar jarrabawa ne, hakuri da juriya shi ke sanyawa a samu nasara.
Na ce: “Ki duba mutane da yawa, wadansu kurame ne; wadansu makafi ne; wadansu guragu ne; wadansu ba sa iya cin abinci saboda rashin lafiya; wadansu ba sa iya tantance kamshi da wari…”
Na ja numfashi wanda hakan ya sanya ta ci gaba da kallona, bayan na kalli idanunta da suka kumbura ne, sai na ci gaba da magana, “…ki duba wadansu ba sa samun abincin da za su ci, amma duk da haka ba su gwammace mutuwa a kan rayuwa ba. Kada ki manta komai ya yi farko yana da karshe. Duk tsanani kuma a gefensa akwai sauki. Kuma ba a tabbata a kan abu daya, dole canji zai zo, inda kuma akan shan dadi bayan an yi jure wa wuya…”
Ta yi ajiyar zuciya, hakan ya sanya na rike hannunta, a lokaci guda na ci gaba da wasa da ’yan yatsunta. Na sake kallonta. Ana cikin hakan sai wani makaho ya zo wucewa, inda yake dogarawa da sanda, a gabanta wadansu jama’a suke yi masa magana kan wurin da zai bi. Hakan ya sanya ta sake yin ajiyar zuciya.
Daga nan na ci gaba da magana: “Komai na rayuwa yana tattare da hakuri kafin a ci nasara. Don haka ki kasance mai hakuri, sannan duk halin da kika kasance idan kina kallon na kasa da ke, ko kuma halin da wadansu suke ciki, to ba za ki taba kasancewa cikin bakin ciki ba. Don haka abin da za ki rika yi shi ne, addu’a, duk mai addu’a na tare da nasara. Mika kukanki ga Allah (SWT), Zai share miki hawayenki.”
Lokacin na farko da na ga ta yi murmushi ke nan. Ta yi mini godiya, sannan muka yi sallama bayan na raka ta zuwa gidansu.
Da wannan nake ba iyaye shawara su sani duk wanda yake karkarshinsu amana ne gare su, kuma za a tambaye su yadda suka rike duk wanda yake karkashinsu. Iyaye masu yin haka, su fahimta idan bayan sun rasu aka yi wa ’ya’yansu hakan za su ji dadi? Na tabbata ba za su ji dadi ba, idan kuwa haka ne me ya sa za su rika gallaza wa ’ya’yan wasu. Ina fata wannan labarin zai zama silar da iyaye masu irin wannan halin za su canza. Allah Ya taimake mu, amin.