✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Labaran rayuwar ma’aurata

Na sha wahalar aure, daga baya Allah Ya saka min da mafi kyawun sakamako!

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. A yau kuma za mu ci gaba da kawo labaran rayuwar ma’aurata kamar yadda suka aiko mana. Kuma kuna iya aiko da na labaran rayuwar aurenku ko taWasaf ko sakon tes.

Na sha wahalar aure, daga baya Allah Ya saka min da mafi kyawun sakamako!

Malama Nabilah ga labarina, da fatan zai amfanar da sauran ma’aurata, musamman mata masu isgili a gidan miji da magidanta da ba su dace da matan aure ba, in suka yi hakuri saboda Allah, Allah zai saka masu da mafi kyawun sakamako.

Da farko na auro matata daga kauyenmu, na kawo ta birni inda nake zaune ina kasuwanci. Muna zaune lafiya har Allah Ya ba mu haihuwar da namiji. Yaron ko shekara bai cika ba, watarana na dawo daga kasuwa na samu gidan a rufe, da jaririn a ciki yana ta kuka.

Abin ya bakanta min rai sosai. Ban fito ba kuma ban neme ta ba har sai bayan wata biyu sannan madaurin auren ya aiko min yana son ganina. Na je garin aka zauna da ni da ita da madaurin aurenta.

Ya tambayi lafiya ya ga iyalina a zaune a gida har tsawon wata biyu. Na labarta masa duk abin da ya faru, na ce ba fada muka yi ba don haka ban san dalilinta na zuwa gida ba sai dai ya tambaye ta.

Da ya tambaye ta, sai ta ce wai yayarta ce ta zo ta ce ta tattara kayanta su taho gida. Madaurin auren nata ya nemi ya sasanta mu, ya ba ni hakuri, na ce da shi da a ce ta taho da yaron nan, da a ce ko makwabta ta mika shi ta ba da ajiya, to da zan iya hakuri in mai da ita.

Amma duk uwar da za ta yi wa dan da haifa a cikinta haka, to abin tsoro ne zama da ita domin komai za ta iya yi. Don haka, na rubuta mata takarda na koma gida.

Na sa abokaina suka taya ni meman mace mai tarbiyya. Bayan auren ta halaye marasa kyau suka yi ta bayyana daga gare ta, mace mara tausayi da yawan isgilanci.

Duk ranar da na bukace ta da ibadar aure sai na bayar da wani abu kafin na samu. Wani lokacin kudi take yanka min, wani lokacin sai na mata alkawarin saya mata wani abu mai tsada ko ta ce sai na fita na siyo mata nama ko ice-cream ko duk wani kayan makulashe da ta bukata.

Ban mancewa wata rana ta bukaci tana son wani kalar balangu na musamman, na fita na je wajen na samu sun tashi, ta ce ai in je na unguwa kaza zan samu, na fita ban samu abin hawa ba, haka na tafi na yi tafiya mai nisan gaske a kasa, shi ma can din ban samu ba.

Na dawo gida dare ya yi nisa sosai. Na dinga rokonta har na duka amma ta ki yarda ta ce tunda ba balangun da take so, ni ma ba zan samu abin da nake so ba. Ta yi kwanciyarta ta yi barcinta ni kuma na yi alwala na fuskanci Ubangijina, ina kuka ina gaya masa damuwata.

Wata shekara Allah Ya ba ni ikon zuwa umara, duk addu’a ta ba ta wuce ta Allah Ya ba ni salihar mace mai kauna ta, wacce ta damu da damuwata.

Wata rana ina zaune a gaban dakin Allah ina ta addu’a a kan bukatuna, sai barci ya dan fige ni haka, sai na yi mafarki an ce min ka kwantar da hankalinka, ga matar da za ka aura nan wacce za ta yaye maka dukkan kuncinka ta bangaren aure.

Bayan na dawo gida sai wani abokina ya hada ni da wata ’yar uwarsa bazawara, amma ba ta taba haihuwa ba. Ina ganin ta sai na ga kamar wacce aka nuna min a cikin mafarki.

Nan da nan magana ta kankama, aka yi aure. Matata ta sa rigima karshe dai aure ya mutu tsakaninmu. Wannan sabuwar matar tana sona sosai zan iya cewa fiye da yadda nake son kaina ma, domin ita ta hada lefen gaba daya, sannan kuma ta kawo wasu ta ce ga tata gudummawar nan.

Bayan amarya ta zo kullum sai zaryar kawo kara salihar matar.Sai na zaunar da ita na ce, tunda kikazo gidan nan wance ba ta taba kawo min kararki ba ko sau daya, amma ke kusan kullum kina min mita a kanta, kin ji irin yadda ta taimaka min wajen aurenki, don haka in kina son zama da ni sai ki yi mata biyayya.

In kuma kin ji ba za ki iya ba, ga hanya nan. Wannan bayani ya sa ta dawo hankalinta aka ci gaba da zama lafiya. Yanzu haka salihar matata ta kara taimaka min wajen kara wani auren, makwabtanmu ne mijin ya rasu ya bar matar da yara biyu, ta matsa min har sai da na nemi auren wannan mata, kuma ta dinga zuwa tana min kanfen har sai da ta amince, yanzu haka ina cikin angwanci na uku.

Don haka, ina kira mazan aure da suke fuskantar muzgunawa daga matan aurensu da su ci gaba da hakuri kuma su dage da addu’a in sha Allah kowane tsanani yana tare da sauki, kuma ina kiran mata masu isgilanci a gidan miji da su ji tsoron Allah su tuba su daina.

Duk fa matar da ta mutu mijinta na cikin fushi da ita, to ba ita ba shiga Aljannah kamar yadda Hadisi ya tabbatar mana. Yanzu ita tsohuwar matata ta koma gidan iyayenta, ta kasa auren ko data daga masu zuwa nemanta don tana ganin ba za ta samu jin-dadi da ta samu a gidana ba. karshe dai ta zo babu ko mai zuwa nemanta, saboda tsufa ya taso mata jikinta ya canza domin ba ta samun irin kulawar da ta saba samu. Don haka, in gemun dan uwanka ya kama da wuta, shafa wa naka ruwa.