✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

La-Liga: Gobe za a yi karon batta tsakanin Real Madrid da FC Barcelona

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi karon batta a tsakanin kulob din Real Madrid da FC Barcelona a gasar rukuni-rukuni na…

A gobe Asabar idan Allah Ya kaimu za a yi karon batta a tsakanin kulob din Real Madrid da FC Barcelona a gasar rukuni-rukuni na La-Liga da ke Sifen.

Wasan, wanda ake wa lakabi da El-classico za a fara shi ne da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya. Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil inda magoya bayan kulob din biyu za su kashe kwarkwatar idanu.
Ana yi wa wasan kirari a matsayin wanda babu irinsa a tarihin kwallo a duk lokacin da kungiyoyin biyu za su hadu. Wasu masana harkar kwallo ma cewa suka yi a duk lokacin da za a gwabza komai kan tsaya cik a fagen kwallo. a fadin duniya.
A halin yanzu dai Barcelona ce take kan gaba a teburin gasar La-Liga bayan ta hada maki 22 daga wasanni 8. Ya zuwa yanzu kulob din bai samu nasara a gasar ba, bayan ya yi nasara a wasanni bakwai sannan ya yi kunnen doki a wasa daya. Sannan kulob din ya samu nasarar jefa kwallaye 22 a raga kuma babu ko kwallo daya da ta shiga ragarsa ya zuwa wannan lokaci. Don haka za a iya cewa kulob din ba karamin tashe yake a gasar ta La-Liga a wannan lokaci ba kuma ya kasance na daya a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar
A bangaren kulob din Madrid kuwa, kulob din ne na uku a teburin La-Ligar bayan ya hada maki 18 a wasanni 8. Ya samu rashin nasara a wasanni biyu daga cikin wasanni takwas. Sannan kawo yanzu kulob din ne ya fi kowane yawan zura kwallo a raga bayan ya zura kwallaye 30 inda shi kuma kaa zura masa kwallaye tara.
Don haka idan kulob din Madrid ya samu nasara a wasan gobe, zai rage saura maki daya kenan a tsakaninsa da na Barca amma idan kulob din Barca ne ya samu nasara zai kara yi wa na Madrid tazara da maki bakwai kenan.
Magoya bayan kulob din biyu musamman wadanda suke nan gida suna ta cacar baki, wasu ma har caca suka yi a kan kulob din da zai samu nasara a wasan.
Ko ma dai ya za ta kasance duniya ta zuba ido ta ga yadda wasan zai gudana.