✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kyankyaso ya makale masa a kunne har kwana 3

Wani dan kasar New Zealand wanda a farko ya yi tunanin ruwa ne ya shige cikin kunnensa ya toshe kunnen da hakan ya tayar masa…

Wani dan kasar New Zealand wanda a farko ya yi tunanin ruwa ne ya shige cikin kunnensa ya toshe kunnen da hakan ya tayar masa da hankali, daga bisani an gano kyankyaso ne mai rai ne ya shige cikin kunnen ba ruwa ba.

Mutumin mai suna Zane Wedding, mai shekara 40, dan garin Auckland ne, kuma ya ce ya yi ninkaya a wani wurin shakatawa a ranar Juma’a inda daga baya ya fara jin kunnensa ya yi dim.

“Na yi amfani da wasu magunguna don rage zafin, sannan na yi barci a daren,” kamar yadda ya bayyana wa kafar labaran na CNN.

Ya ce, kunnen nasa ya toshe zuwa washegari, don haka ya je ya ga likita, wanda ya ba shi shawarar ya yi kokarin amfani da na’urar busar da gashi wajen busar da ruwan da yake cikin kunnen.

Zane ya ce, abin ya ci tura don haka ya je ya ga likitan kunne da hanci da makogwaro. Ya ce, likitar ta bayyana kaduwarta nan take da ta duba cikin kunnen.

“Ta ce: ‘Ina tsammanin akwai kwaro a cikin kunnenka,” Zane ya bayyana wa jaridar New Zealand Herald, inda ya ce, ya dauki kusan minti biyar likitar tana cire kyankyason.

“Duk lokacin da ta taba shi, sai in yi tunanin ta ina kyankyason ya shiga cikin kunnena? Don haka ban samu natsuwa ba,” inji shi.

Ya ce, ya samu “sauki nan take” lokacin da kwaron ya fito. Ya ce, “Na ji wani kuka lokacin da aka cire shi.” Ya ce, shigar kwaron ta sa ya dada kyamar sauran kwari.

“Har yanzu kunnen yana min radadi,” inji shi.