Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu amfani da kyallen rufe fuska ya zama wajibi ga dukkan ‘yan Najeriya a matsayin matakin kariya daga cutar coronavirus.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin jawabin hadin gwiwa a kan annobar karo na 31 a Abuja.
Ya ce daga yanzu amfani da kyallen wajibi ne ba ganin dama ba, tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar hana yaduwar cutar hannu.
Mista Mustapha ya kara da cewa matakin na cikin hanyoyin da ake amfani da su don kare kai daga kamuwa da cutar, yana mai kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da bin dokar.
Hakazalika, ya yi kira ga gwamnonin Najeriya 36 da su tabbatar da bin dokar a jihohinsu.
Ya ce, “Amfani da kyallen na cikin tanade-tanaden kudurin dokar yaki da cutar da Shugaba Buhari ya sanyawa hannu.
“Saboda haka, matukar shugaba ya sanya wa doka hannu, to ya zama wajibi a yi mata biyayya.
“Kiran mu ga alu’ummar Najeriya shi ne su ci gaba da ba mu hadin kai wajen bin wannan umarnin.
“Ba dole ne sai wanda jami’an lafiya suka amince da shi za a iya amfani da shi ba, ko kyalle mutum ya sa matukar ya kare fuskarsa ma ya wadatar.
“Yana da kyau mu kiyaye wannan doka da kuma sauran dokokin lafiya don amfanin kan mu”, inji Boss Mustapha.
Gwamnoni sun bi sahu
Wakilanmu sun rawaito cewa da yawa daga cikin gwamnonin Najeriya da ma Ministan Babban Birnin Tarayya ma sun bi sahu wajen saka wannan dokar.
Alal misali, a farkon makon nan, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da kafa makamanciyar wannan doka a jihar Kano, yana mai cewa akwai tara a kan duk wanda aka kama ba ya amfani da kyallen.
Har ila yau, jihar Legas ma a ranar 25 ga watan Afrilu ta bi sahu.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya ce an yi kwakkwaran tanadi wajen ganin an samar da kyallayen da yawa ta yadda za su wadatar da al’ummar jihar.
Rahotanni dai sun nuna cewa tun da farko gwamnonin ne suka rubuta wa Shugaba Buhari wasika suka bayar da shawarar kafa wannan dokar a duk fadin kasa.
Mai dokar bacci…
To sai dai kuma Aminiya ta gano cewa a ‘yan kwanakin nan Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taruka har sau biyu ba tare da amfani da kyallen ba.
A ranar Larabar da ta gabata, an hangi shugaban kasar ba kyallen yayin taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, duk da cewa mataimakinsa da sauran mukarrabansa suna sanye da shi.
Bugu da kari, yayin taronsa da manyan hafsoshin tsaron kasa ranar Alhamis, shugaban kasar bai yi amfani da kyallen ba, duk kuwa da umarnin da ya bayar a kan haka a jawabinsa ga kasa na karshe kan cutar ta corona.
Kin amfani da kyallen
Dokta Ndubuisi Onuoha, wani kwararre a kan cututtuka masu alaka da numfashi, ya ce kin yin amfani da kyallen na shugaban kasa da ma wasu manyan jami’an gwamnati karan-tsaye ne ga dokokin lafiya kuma zai iya jefa wasu cikin hadarin kamuwa.
Ya ce kamata ya yi idan mutum ba ya son saka kyallen, to ya yi zaman shi a gida.