Hukumar Kwastam ta kama wata tankar mai makare da buhunan shinkafar kasar waje da motar ke fasakwurin ta a Jihar Katsina.
Da yeke gabatar da kayan, Kwanturolan Kwastam mai kula da shiyyar Katsina, Adewale Musa Aremu, ya ce masu faskwaurin sun boye buhunan shinkafar waje 210 a cikin biyu daga cikin mazubai uku na tankin.
- Ba’amurkiyar da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu
- ’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Geidam
- Tsohon Sarkin Kano ya magantu kan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Abduljabbar
Kwanturola Aremu ya ce jami’an Hukumar sun tsare motar ce a Dutsinma bayan samun bayanan sirri cewa fasakwaurin shinkafa motar take yi, tana batar da sawu da man fetur.
Ya ce mutanen da ke cikin motar da aka yi wa jabun takardun shaidar kamfanin mai na A.A. Rano na can a tsare taer da wani wanda ya zo yana ikirarin cewa motar tasa ce.
Kwanturolan ya ce bayan kammala bincike za a gabatar da su domin daukar matakin da ya dace da masu aikata fasakwauri.
Ya ce reshen Hukumar ya kuma kama motocin da aka yi fasakwaurinsu da kudinsu ya kai Naira miliyan 32, ciki har da tankar da aka kamar wajen a cikinta.