✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama wukake da tabar wiwin N10.4m a Kaduna

Jami'an Kwastam sun kama wukake kirar kasashen waje 60 da kunshi 250 na tabar wiwi a Kaduna.

Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama kananan wukake kirar kasashen waje guda 60 da kuma kunshi 250 na tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira miliyan 10.4 da aka yi fasakwaurinsu a Jihar Kaduna.

Kwanturolan Hukumar Kwastam na Rukukin B da ke Kaduna, Albashir Hamisu, ya ce kananan wukaken da aka yi fasakwauri suna da matukar hadari, don haka za a hannanta su ga hukumar ’yan sanda.

A cewarsa, ita kuma tabar wiwin, da an yi sake ta shiga gari, bata-gari ne za su rika amfani da ita domin aikata laifuka a jihar.

Saboda haka ya bukaci Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da ta gudanar da bincike domin gano inda ake samo tabar wiwin da kuma cafke masu masakwaurinta zuwa Najeriya.