Hukumar Kwastam a Najeriya (NCS) ta bayyana kwato tabar wiwi da ta kai kimanin naira miliyan 516 a gabar tekun Legas.
Kwanturolan NCS a gabar tekun, Sani Yusuf, shi ya bayyana hakan a ranar Laraba a Legas yayin zantawa da manema labarai.
- ‘Abba Kyari ya yi min tayin N10m don na yi wa Saraki kazafi’
- Faransawa na bore kan sake fasalin fansho
Yusuf ya ce an kwato tabar wiwi da ta kai nauyin kilo 5,124 ne bayan samun bayanan sirri.
Ya kara da cewa an dauko tabar ce daga jirgin ruwa zuwa manyan motoci da nufin tafiya da su wani wuri kafin jami’ansa su dirar musu.
Ya kuma ce a dan tsakanin nan, tawagarsa ta kuma kwato jakukkuna 705 na shinkafar kasar waje mai nauyin kilo 50 wadda aka biya kudin shigo da ita kan naira miliyan 42 da kuma tarin tufafi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito Kwanturolan na cewa tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022, sun samu nasarar kwato kayayyakin da aka haramta shigo da su daban-daban wadanda kuma kudinsu ya kai naira biliyan 9.
Ya gargadi masu shigo da kayayyakin da su daina abubuwan da suke yi, inda ya ce daga yanzu ba kaya kadai hukumar za ta kwato ba, har ma da kama masu take doka domin su fuskanci hukunci.