Hukumar Kwastam ta kama wasu kayan gwanjo da kwayoyi da aka shigo da su ta barauniyar hanya Jihar Kano.
Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana na yaki da Fasakaurin, O. A, Olurukoba ya ce kayan da kimarsu ta kai Naira miliyan 20 ne an kama su ne a ranar Talata.
- An dawo da kayan tallafin COVID-19 da aka yi warwaso a Filato
- Direba ya cika bujensa da iska bayan kashe wata mata a titi
- Dan sanda ya harbe dan Achaba kan N50
Olurukoba ya ce galibim kayan an shigo da su ne daga kasashen da cutar COVID-19 ta yi wa katutu, wanda ya ce abun takaici ne shigo da irin kayayyakin a daidai lokacin da ake kokarin kayar COVID-19
Shugaban ya ce, hukumar ba za ta yi kasa a guiwa ba wurin yaki da masu safarar kowane irin kaya ta barauniyar hanya.
Olurukoba ya ci gaba da cewa, hukumar a shirye take ta bi ko’ina a fadin Jihar Kano domin kwace kayan da aka yi fasakwarinsu daga wani wuri zuwa jihar.
Ya ce yanzu sun daina kwace kaya kawai, sai an hada da tsare mai su a kuma gurfanar da shi a kotu kan laifin da ya aikata na karya doka.