Hukumar Kwastam ta kama wani sunduki makare da kasusuwan dabobbi da suka hada da na zaki da hauren giwa da bawon dabbar Pangolin da kudinsu ya kai Naira biliyan daya.
Kwanturolan Hukumar na Apapa, Muhammad Abba Kura ne ya bayyana hakan yayin gabatar da kayayyakin da hukumar ta kama a tashar jiragen ruwa ta Apapa, inda ya ce an yi yunkurin ketarewa da kayayyakin ne daga Najeriya zuwa kasar Vietnam.
- Maciji ya kashe mutum 7, 15 sun kamu da ciwon kafa
- Karamin yaro ya salwantar da N1.2m a wayar uwarsa
- Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa
Abba Kura yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Talata ya ce, hukumar ta kama kayayyakin ne bayan binciken hadin gwiwar da ta yi da takwarorinta na kasashen waje.
Ya ce: “Bayanan sirrin da suka tattaro ne ya sa suka sa ido kan duk kayan da ake yunkurin fita da su zuwa kasashen Asiya, kuma sun shafe kusan shekara suna wannan aiki.”
Hukumar Kare Dabbobin Daji ta Duniya ta hana farautar Pangolin, sai dai an gano cewa masu fasa kwaurin dabbar suna amfani da tekun Najeriya wajen shigowa da fitar da irin wannan kayan zuwa kasashen duniya da suke sarrafa bawon Pangolin wajen hada sulke.
Dabbar Pangolin tana cikin dabbobin da suke fuskantar barazanar karewa a duniya wanda hakan ya biyo bayan rububin farautarta da fataucinta a kasashen duniya ne.
Bincike ya ce kasar China ce kan gaba wajen hada irin wannan sulke da magungunan gargajiya da sassan wannan dabba tana sayarwa da tsada.
Asirin masu fasa kwaurin Pangolin din ya fara tonuwa ne a Legas lokacin da Hukumar Kwastam ta gabar tekun Apapa ta kama wata kwantaina dauke da bawon Pengolin mai nauyin kilo 8,800 da hauren giwa da kasusuwan zaki a watannin baya.