✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta bukaci manoma su karfafa noman shinkafa a Katsina

Hukumar ta ce hakan zai hana shigo da ta waje

Hukumar Kwastam ta shawarci manoman Jihar Katsina su dukufa wajen noman shinkafa maimakon amfani da ta waje.

Hukumar ta ce, hakan zai kara habaka hanyoyin samar da ayyukan yi da kuma bayar da damar janyo ’yan kasuwa daga wajen maimakon kai masu kudaden kasar nan.

Kwanturolan Hukumar a Jihar Katsina, Alhaji dalha Wada Chedi ne ya shawarci manoman a lokacin da yake gabatar wa manema labarai nasarorin da hukumar ta samu wajen dakile ayyukan fasa-kwauri da wasu ke yi a jihar.

Ya nuna takaici game da asarar dukiyar da ake yi dalilin fasa-kwauri, “Yanzu a ce an shigo da shinkafar da aka kama akalla buhu 447 wadda kudinta ya haura Naira miliyan 12, ba karamar asara ba ce tare da gurgunta tattalin arzikinmu, domin da a nan cikin gida aka yi amfani da kudin da an kara habaka harkokin noman shinkafar har kasashen waje su rika shigowa suna saye daga hannun manoma.

“A nan Jihar Katsina akwai wuraren noman shinkafa irin su dandume da Faskari da Funtuwa da danja da Bakori da irin su madatsar ruwa ta Sabke da ke yankin Mai’aduwa da kuma yankin Jibiya. Dukkansu wurare ne na noman shinkafa wadda ta fi wadda ake shigowa kyau da inganci,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Idan batun wajen gyara shinkafar ce baya ga Jihar Zamfara da makwabtan jihar, Jihar Katsina tana da wuraren da ake gyara shinkafar. Ya ce, “Akwai wajen gyara shinkafa a hanyar zuwa Jibiya daga Katsina, akwai a hanyar zuwa Dutsinma da ita kanta Dutsinmar, ga can wajen su Faskari da sauransu.”

Hukumar ta ce ta kama kayan abinci irin su man Olga da taliya da fulawa da sauransu da kudinsu ya kai Naira miliyan 73 da dubu 675. Sai motoci manya da kanana da kudinsu ya haura Naira miliyan 45.

Sai dai Kwanturolan ya ce, duk da matsalar tsaro musamman a hanyar Jibiya ta haifar da cikas ga manoma wajen samun kudaden shiga, duk da haka ya yi kira ga masu safara a tsakanin kasashen su ci gaba da bin ka’ida ta hanyar biyan kudin da suka dace don shigowa da kayansu maimakon bin barauniyar hanya.