✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta ba da wa’adi ga mai motocin alfarama ya bayyana kansa

Hukumar Kwastam a Jihar Sakkwato ta ce motocin alfarma da ta kama za su iya zama na Gwamantin Tarayya matukar mai motocin bai bayyana kansa…

Hukumar Kwastam a Jihar Sakkwato ta ce motocin alfarma da ta kama za su iya zama na Gwamantin Tarayya matukar mai motocin bai bayyana kansa ba cikin kwana 30. Ta bukaci ya hanzarta bayyana kansa da cikakkun takardun biyan harajin shigo da motocin don kauce wa fuskantar hukunci.

A taron manema labarai da hukumar ta kira Kwanturola Alhaji Nasir Ahmad ya yi kira ga mutane su daina yada jita-jita kan motocin ana cewa motocin sun kai 160, ya ce motoci 48 ne ke hannunsu kuma ba su ce na wani babban dan siyasa ne domin har yanzu ba wanda ya ce nasa ne. Sannan motoocin ba a gida ne suka kama su ba a wani kangon fili ne.

Ya ce kudin harajin motocin 48 gaba daya, manyan Jeep 20 da Toyota Avensis 28, Naira miliyan 196 ne ya kamata a biya.

Kwanturola Ahmad ya ce hukumar ta ara kudin shiga Naira miliyan 443.7 a zangon farko na bana savanin Naira miliyan 368.8 a bara. Kuma sun kama jarkar mai sama da 2000 da buhun shinkafar waje 527, sai kuma harajin fiton motoci sama Naira miliyan 412 da miliyan 6.6 a jere 

Shugaban masu sayar da motoci na Jihar Sakkwato Alhaji Muntari Mafiya ya shaida wa wakilnmu cewa motocinsa ne duka kuma ya sanar da hukumar, hasali ma shi ya ba su makullan motocin lokacin da suka zo kwasar su, amma sai ga shi hukumar ta ce ba wanda ya zo ya ce nasa ne.