✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam sun sake kama motocin alfarma a Legas

Motocin alfarma guda 31 masu darajar fiye da Naira biliyan daya da miliyan 400  da aka shigo da su cikin kasar nan ba tare da…

Motocin alfarma guda 31 masu darajar fiye da Naira biliyan daya da miliyan 400  da aka shigo da su cikin kasar nan ba tare da biya musu harajin fito ba sun fada hannun Hukumar Kwastam da ke Ikeja a Legas. 

Hudu daga cikin motocin, kirar Rolls Royce ne da aka kera su a bara. Da yake nuna wa ’yan jarida motocin a makon jiya, Kwamandan Hukumar, Kwanturola Muhammed Uba Garba ya bayar da wa’adin wata daya ga mutanen da suka mallaki motocin, “Su zo da cikakkun takardun halaccin mallaka da biyan kudin harajin fito ga gwamnati, domin karbar motocin, kuma idan suka kasa hakan zuwa karshen wa’adin wata daya to, motocin za su zama mallakar gwamnati, kamar yadda doka ta tanada.”

Ya ce “Mun kama motocin ne a kan babbar hanyar Ijebu Ode da rukunin gidaje na Parbiew da bictoria Isand da Banana Island da Ikeja da Maryland duk a Legas. Mun yi amfani da labarin musayar ra’ayi a tsakaninmu da wadansu mutane masu kishin kasa da suka ba mu labarin wuraren da aka boye motocin.” 

Ya kara da cewa: “Bayan wadannan motoci, akwai buhunan shinkafa 8,400 da katan 1, 652 na naman kaji da talo-talo da jarkoki 835 na man girki da tayoyin mota 2, 208 da daurin gwanjo 159 da buhunan wiwi 10 a sassa daban-daban na sashen Kudu maso Yamma. Duka motoci da kayan mun yi nasarar kama su ne a tsakanin 1 zuwa 31 ga Janairun bana.”

Kwanturola Garba ya roki  kafofin labarai su ci gaba da bayar da labaran da za su taimaka wa bunkasa tattalin arzikin Najeiya. “Domin wannan aiki ne da kowannenmu zai bayar da gudunmawarsa domin gina kasar haihuwarsa,” inji shi.