Jami’an Kwastam reshen Jihar Jigawa sun harbi mutum biyu da bindiga, inda a sakamakon haka daya mai suna Alhaji Umaru na garin Babban Mutun da ke Jihar Katsina ya rasa ransa.
Mutumin, wanda ake zaton yana daya daga cikin mutanen da suke hada kai da jami’an Kwastam wajen shigowa ko fita da kayan abinci daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar, a harbe shi ne a gadon baya, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibitin garin babura domin ceto ransa amma daga bisani ya rasu. A yayin da daya mutumin da aka harba a kafa, mai suna Iliyasu Usman aka kai shi Asibitin Malam Aminu Kano, inda yake jinya.
Aminiya ta kalato cewa, ganin yadda jami’an na Kwastam suka bude wa mutanen biyu wuta a bainar jama’a ya sa mutanen gari suka kai masu farmaki, inda suka kone motocin hukumar guda hudu, yayin da jami’an suka gudu.
Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Kakakin Hukumar Kwastam mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Malam danbaba ya ce al’amarin ya faru amma ba shi da sahihan bayanai cikakku da zai wa manema labarai bayani, sai dai a jira shi zuwa lokacin da za su kammala bincike daga baya zai yi wa manema labarai karin haske.