✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwastam sun kama shinkafa da daskararrun naman kaji da talo-talo a Legas

Rundunar kwastam ta FOU da ke Ikeja, a Legas, ta yi nasarar kama wata babbar mota dauke da katon dubu daya da 74 na daskararrun…

Babbar motar da ke dauke da daskararrun naman kaji da talo-talo ke nan.Rundunar kwastam ta FOU da ke Ikeja, a Legas, ta yi nasarar kama wata babbar mota dauke da katon dubu daya da 74 na daskararrun naman kaji da talo-talo da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 5 da dubu 799 da kuma wata babbar mota dauke da buhunan shinkafa da aka kiyasta kudinta ya kai Naira miliyan 16 da dubu 500 da aka shigo da su ta haramtacciyar hanya.
Da yake nuna kayayyakin, Kwamandan rundunar ta FOU, Kwanturola Nuhu Isa Mahmoud ya ce, an samu nasarar kamun kayan ne lokacin da Mataimakin Kwanturola Abdullahi Kiyawa ya jagoranci jami’an hukumar zuwa wani samame inda aka kama mutum biyu direban motar mai suna Mike Abram da Mista Richard Ikhabuzor da ke rakiyar kayan.
Ya ce babbar motar kirar DAF mai lamba DELTA dB 434 DSZ, an kama ta ne a kan hanyar zuwa kasuwar duniya ta Alaba daga Mil 2, bayan samun labari daga wasu masu kishin kasa.
Kwanturola Mahmoud ya ce, masu kayan sun yi amfani da katon-katon guda 190 na kwalayen madara na biju da Bobo da suka lullube daskararrun naman a ciki domin badda-kama, amma asirinsu ya tonu kafin su kai ga nasarar yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya. Ya nuna matukar farin cikinsa da irin ayyukan da jami’an rundunar suke gudanarwa, wanda ya yi daidai da umarnin Kwanturola-Janar, Abdullahi Dikko Inde.
Ya bayar da tabbacin cewa, “rundunar FOU, za tayi dukkan abin da take iyawa wajen ganin ta fatattaki ’yan sumoga daga cikin shiyyar Kudu maso Yamma.” Ya ce za a gurfanar da mutane biyun da aka kama gaban kotu da zarar sun kammala bincike.   
Har ila yau, Kwanturola Mahmoud, ya jinjina wa tawagar manyan jami’an kwastam na kasa a karkashin jagorancin Kwanturola-Janar Abdullahi Dikko Inde, saboda irin goyon baya da hadin kai da suke bayarwa ga rundunar ta FOU, wanda ya kai ta ga samun nasarori a wannan sashe na kasa. Ya ja kunnen masu fasa kwauri da su tattara nasu ya nasu su kaurace wa sashen Kudu maso Yamma ko kuma su yi wa kansu kiyamul laili su dawo daga rakiyar miyagun ayyukan da suke yi domin a tafi tare wajen samar wa kasa ci gaba da bunkasar tattalin arziki.