✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ni zan lashe zaben shugaban kasa —Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kada kuri'arsa a mazabarsa

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana da yakinin cewa shi zai lashe kujerar shugaban kasa na ranar Asabar.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabarsa a rumfar zabensa ta Kwankwso Malamai da ke Kamara Hukumar Madobi a Jihar Kano.

Ya bayyana cewa,m “Ai Gani ya kori ji. Daga yadda kuka ga irin yadda mutane suka fito suka kuma dage akan bukatarsu to wannan ya isa ya bayyana maka inda nasara take. A bayyane take mu ne za u yi nasara da yardar Allah.”