✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Kwankwaso ya jajentawa Pillars

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya jajentawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a bisa tare su da ’yan fashi da makami suka…

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya jajentawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a bisa tare su da ’yan fashi da makami suka yi a Abuja a kan hanyarsu ta zuwa Owerri a ranar Alhamis ta makon jiya inda wasu daga cikin ’yan kwallon suka ji mummunan raunuka.

Gwamnan ya kai ziyarar jejen ce a ranar Lahadin da ta gabata asibitin Malam Aminu da ke Kano inda aka kwantar da ’yan kwallon.
’Yan kwallon da aka harba kuma aka yi nasarar cire musu harsashi a sassan jikinsu a asibitin sun hada da Gambo Mohammed da Otakpa Oneji da kuma Adamu Murtala.
Gwamnan ya bayyana al’amarin da ya faru a matsayin abin takaici ganin cewa ’yan fashin sun far wa ’yan kwallon da jami’ansu ne babu gaira, kuma babu dalili.
Gwamnan ya zagaya asibitin ne tare da tawagarsa da suka hada da Kwamishinan kula da kiwon lafiya na Jihar Kano Abubakar Yusuf da kuma jami’an kulob din na Pillars. Kwankwaso ya ce ya dauki nauyin kudin jinyar ’yan kwallon. Ya yi musu addu’ar Allah Ya ba su lafiya kuma Allah Ya kare aukuwar irin haka a gaba.