Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran akidar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wata sabuwar makaranta da ya ginawa makiyaya a garin Munture na karamar hukumar Rano a jihar Kano.
Kaddamar da ginin wanda ya gudana a harabar makarantar ranar Talata na daya daga cikin jerin abubuwan da aka tsara gudanarwa domin bikin cikarsa shekaru 64 a duniya da zai yi ranar Laraba.
- 2023: Matasan APC sun roki Atiku da Kwankwaso su dawo
- Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagayowar haihuwarsa
Makarantar dai wacce Gidauniyar Kwankwasiyya ta gina ta kunshi azuzuwa shida kuma za ta dibi akalla dalibai 300, yawancinsu ‘ya’yan Fulani makiyaya dake yankin.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da makarantar, Sanata Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar daga likkafar makarantar ne daga ta Islamiyya zalla ta hanyar gina ta domin samarwa da mazauna yankin ingantaccen ilimi.
Kwankwaso wanda kuma tsohon sanata ne da ya wakilcin Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta takwas ya ce yana da kudurin ganin ya tallafawa ilimin yaran yankin har zuwa matakin jami’a.
A cewarsa, “Babban buri na shine na ga na samarwa da al’umma ilimi, musamman ma ‘ya’yan talakawa saboda ta hanyar ilimantar da jama’a ne kawai za ka iya ceto su daga duhun kai, wannan kuma ita ce akidar tafiyarmu.
“Wannan makaranta ta jima sosai amma a matsayin ta Islamiyya zallah. Sai muka ga ya dace mu gina musu ita domin ta bayar da ilimin boko da na Islamiyya,” inji shi.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar yankin da su yi amfani da makarantar yadda ya kamata ta hanyar tura yaransu cikinta da kuma kula da ita domin amfanin yankin gaba daya.
Da yake tsokaci a yayin bude makarantar, shugaban Kungiyar Miyetti-Allah Kautal Hore ta Kasa ya jinjinawa tsohon gwamnan saboda karamcin da ya yi wa yankin, yana mai cewa za ta taka muhimmiyar rawa wajen kawar da jahilci.
Taron dai ya sami halartar dubban mabiya akidar ta Kwankwasiyya daga sassa daban-daban na jihar ta Kano.