✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP

Kwankwaso ya fitar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar a ranar Talata

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’yyar PDP.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Idan ba a manta ba, Sanata Kwankwaso ya jima yana shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar, tun bayan kafa tafiyar siyasa ta TNM.

A ranar Lahadi ce, daya daga cikin jagororin darikar Kwankwasiyya kuma na gaban goshin Kwankwaso, Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida), ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP, mai alamar kayan marmari.

Abba Gida-gida dai ya zargi jam’iyyar PDP da gaza bai wa bangaren na Kwankwasiyya dama, duk da irin halarcin da su kai wa jam’iyyar a zaben 2019.

Ana sa ran Kwankwaso zai tsaya takarar Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar NNPP, a babban zaben 2023 da ke karatowa.