Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP ya lashe zaben shugaban kasa a Jihar Kano da kuri’a kusan miliyan daya.
Kwakwaso ya yi nasara ne bayan ya samu gagarumin rinjaye da kuri’a 997,278, inda ya ba wa manyan abokan hamayyarsa gagarumin tazara, kamar yadda baturen zaben kuma Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Lawan Suleiman Bilbis, ya sanar a ranar Litinin da dare.
- Duk da goyon bayan Ortom ga Obi, Tinubu ya lashe Binuwai
- Zaben shugaban kasa: Atiku ya yi nasara a Jihar Neja
Sakamakon zaben ya nuna Kwankwaso ne ya yi nasara a 36 daga cikin kananan hukumomi 44 da ke fadin Jihar Kano.
Ya bayyana cewa, wanda ya zo na biyu shi ne dan taarar Shugana kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda ya samu kuri’a 517,341, wanda Kwankwaso na NNPP ya ba wa tazarar kuri’a 479,000.
Wanda ya zo na uku shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na PDP da ya samu 131,604 sannan Peter Obi na LP ya tashi nda 28,522.