Gwamnatin Kano ta ce tsohon Gwamnan Jihar, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bar mata bashin fiye da naira biliyan hamsin na aikin gina titin kilomita biyar-biyar a Kananan Hukumomi 44 da ke fadin Jihar.
Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Muhammadu Sanusi Kiru ne ya bayyyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi yayin ganawarsa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Kano.
- Mayakan ISWAP sun kashe mutum hudu a Borno
- Saudiyya ta rage yawan raka’o’in sallar dare a Masallatan Harami
Sanarwar hakan na zuwa ne a yayin da Kwamishinan ya zayyana wa manema labarai batutuwan da suka tattauna yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar a makon da ya gabata.
A cewarsa, Majalisar ta gano hakan ne bayan karbar rahoton kwamitin kwararru da suka bibiyi kwangilar gina titunan a Kananan Hukumomi 39 karkashin Hukumar tsara birane ta Jihar, KNUPDA.
Sai dai ya ce an karbe aikin Kananan Hukumomi uku da suka hada da Warawa, Ungogo da Dawakin Tofa, sai kuma wani tsagi na aikin Tsanyawa da Bichi, inda aka mayar da kwangilar hannun Gwamnatin Tarayya yayin da ta bukata.
Kazalika, ya ce an sauya wuraren da aka bayar da aikin kwangilar Kananan Hukumomin Bunkure, Rimin Gado da Karaye, sannan kuma aka sauya ayyukan Kananan Hukumomin Dala, Nassarawa, Gwale, Tarauni zuwa wasu ayyukan na daban a madadin gina titunan.
A nasa martanin, Kwankwaso ta bakin tsohon Kwamishinansa na Ayyukan Cikin Gida kuma dan takarar mataimakin Gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce Ganduje ne ya kamata ya yi bayani dalla dalla a kan wannan zargi.
“Muna godiya ga Allah da ya sanya Ganduje ne Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi kuma shi ne mai kula da duk kwangilar aikin.
“Ma’aikatar Ganduje ce ke kula da ayyuka sannan ita ce mai bayar da shawarwarin biyan kudade ga ’yan kwangila.
Aminu Gwarzo ya yarda cewa galibin ayyukan ba a kammala su ba, sai dai ya ce abin da gwamnatin Kwankwaso ta yi shi ne biyan kashi 30 cikin 100 na kudaden ga ’yan kwangila domin su fara aiki.
“Da farko an biya ’yan kwangila kashi 30% na kudaden a matsayin somin tabi amma duk wanda ya karar da su, sai ya nuna hujjarsa ta cewa ya fara kwangilar ta fiye da wannan kudade da aka ba shi sannan a kara masa, kuma duk wannan ya faru ne a ma’aikatar da ke karkashin jagorancin Ganduje.
“Saboda haka ba mu da wata masaniya a kan bashin naira biliyan hamsin da hudu, watakila wata kitimurmurar ce suke kullawa,” in ji shi.
Gwarzo ya ce gwamnatin Kwankwaso ta gudanar da nata binciken a kan ayyukan gabanin mika wa Ganduje mulki, kuma tana iya gabatar da duk wani rahoto a kai matukar akwai masu kalubalantar ta a kan hakan.