Jam’iyyar NNPP ta musanta cewa dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso na tattaunawa da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar kan goya wa takararsa baya a zaben da ke tafe.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun kwamitin yakin neman zabenta, Ladipo Johnson a ranar Laraba a Abuja.
- ICPC ta kama matar da ke sayar da sabbin kudi a Twitter
- Wike ya hana Atiku wurin taron yakin neman zabe a Ribas
Johnson ya ce a bayyane yake cewa Kwankwaso ya fi Atiku farin jini da kuma iya salon neman mulki.
Ya ce, wannan ya nuna Atiku na neman inda zai rabe, ganin cewa ba zai iya cin zabe ba.
Ya ce sanarwar na da matukar muhimmanci saboda Atiku ya ce dan takarar nasu na tattaunawa da shi don duba yiwuwar yadda zai mara masa baya.
“Magana ta gaskiya ita ce babu wani lokaci da aka yi wata tattaunawa tsakanin Atiku da Kwankwaso, ko kuma wasu daga cikin wakilansu.
“Sau daya suka hadu, lokacin taron ’yan takara a baya.
“Idan ’yan Najeriya ba su manta ba a baya cewa ake yi Kwankwaso ba shi da wani tasiri sai a Kano.
“Mun shigo wannan tafiya ne don sauya yanayin da Najeriya ke ciki, don mu inganta tare da ceto mutane daga halin kunci.
“Abokan hamayya sun ga irin tsarin tafiyar Kwankwaso da yadda mutane ke mararin zabar sa saboda tsari da tanadi da ya zo wa da ’yan Najeriya, shi ya sa kowa ke son zabar NNPP,” in ji shi.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa yana tattaunawa da Kwankwaso da Obi don ganin wani daga cikinsu ya mara wa tafiyarsa baya.