‘Yan Kwankwasiyya a jihar Kano sun soki lamirin Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje na yunkurin rushe gadar da Rabiu Kwankwaso ya gina.
Wannan na kunshe ne cikin wani jawabi da tsohon Kwamishinan Ayyuka lokacin mulkin Kwankwaso, Kwamared Aminu Abdusalam ya fitar a ranar Juma’a.
- Ana bincike kan yadda aka zane wasu ’yan mata da bulala a Bauchi
- COVID-19: Gwamnatin Kano ta raba takunkumi 10m kyauta
Sanarwar ta ce, “Mun ga yadda Gwamnatin Ganduje ta zama annoba ga Kanawa. A ranar 9 ga Fabrairu, aka wayi gari Kwamishinan Ganduje ya sanar da yunkurin Gwamnatin tasu na rushewa tare da sake gina gadar Kofar Nassarawa.
“Idan ba a manta ba a babban zaben 2019 mutanen Kano sun yi kokarin kada Ganduje.
“Amma abin da ya biyo baya ya zama murdiya tun daga kotun daukaka kara har zuwa kotun koli.
“Abin takaici ne cikin shekaru biyu yadda Gwamnatin Ganduje take rushe wurare masu dimbin tarihi suna sayar wa mutane.
“Mun ga yadda take rushe wurare masu muhimmanci tana sayar wa wanda suke da kudi.
“Mun ga yadda Gwamnan ya rushe tashar mota ta zamani a Shahuci, Sansanin Alhazai, Gidan Rediyo na Tukuntawa, Filin Idi na Kofar Mata, Gidan Jaridar Triumph, da sauran wurare.
“A baya-bayan nan ma gwamnan sai da ya yi yunkurin sauya wa gidan Ajiyar Namun Daji da yake da tarihin sama da shekaru 50 wuri saboda ta sayar da filin.
“Akwai kayayyaki da wuraren jama’a da dama da wannan Gwamnati ke saida wa ba bisa ka’ida ba.
“Babu gaskiya a batun cewa gadar Kofar Nassarawa ta fara rushewa. Magana ta gaskiya shi ita ce, Gwamnan na son rushe ta domin ya sayar da filin ga wanda yake da kudi,” cewar Kwankwasiyya.
Daga nan sai Kwankwasiyya ta sha alwashin dawo da duk wata kadara ta Ganduje ya sayar ba bisa ka’ida ba, da zarar ta karbi mulki a 2023.
Fadan Kwankwasiyya da Gandujiyya ya faro ne tun karshen shekara ta biyu a mulkin Ganduje.
Hakan ya sanya Gwamnatin cire ba da umarnin goge sunan Kwankwasiyya daga kan dukkan wasu ayyuka da gwamnatin ta yi a baya.