✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwanan nan mata za su raba Kano da shara – Zubaida Abubakar Damakka

Barista Zubaida Abubakar Damakka ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Al’amuran Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kano.  A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana irin aikace-aikacen da…

Barista Zubaida Abubakar Damakka ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Al’amuran Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kano.  A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana irin aikace-aikacen da suka bullo da shi, don tallafa wa rayuwar mata inda ta ce a kwanan nan Kano za ta canja kasancewar sun bullo da shirin Kano kal- kal wanda mata za su rika kwashe shara a gida-gida:

Tarihin Rayuwa:
Sunana Barista Zubaida Abubakar Damakka. Sunan mahaifina Alhaji Sharif Lawal Adam wanda aka fi sani da Karo da goma. An haife ni a Unguwar Gwammaja a yankin karamar Hukumar Dala cikin Jihar Kano. Na yi karatun firamare a Makarantar Firamare ta Dala. Bayan na gama sai na tafi Kwalejin Kimiyya ta Gwaram inda na yi aji uku na karamar sakandare, daga nan  sai na tafi Kwalejin Kimiyya ta Taura. Daga nan sai na tafi Jami’ar Bayero na karanta harkokin aikin lauya. Bayan na kammala sai na tafi Kwalejin horar da lauyoyi da ke Abuja. Bayan na gama wannan makaranta sai na fara aiki a Abuja a wata cambar lauyoyi ta Abdul And Partners. Sai dai ban dade a wannan wuri ba sai na dawo gida Kano inda nake taimaka wa maigidana wajen harkokin kasuwancinsa. A yanzu haka ya bude kamfaninsa na gidan gona inda muke harkar madara da nono da ice cream da sauransu. Muna cikin hakan ne kuma Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya dauko wananan mukami ya ba ni a matsayin Kwamishinar ma’aikatar Mata ta Jihar Kano.
Iyali:
Ina da aure da ’ya’yanmu shida ni da abokiyar zamana. Ita tana da uku ni ma ina da guda uku. Babbar ’yarmu shekarunta goma sha takwas a yanzu haka tana jami’a. Sauran yaran kuma wadansu suna sakandare yayin da wasu kuma suke firamare.
Nasarori:
Alhamdulillahi zan iya cewa a rayuwa na samu nasara tun daga kan damar karatu da na samu na yi. duk da cewa mahaifina ba mai kudi ba ne, amma ya yi iya kokarinsa wajen ba ni ilimi. Nakan tuna a lokuta da dama yakan ce shi dai ba shi da tarin dukiya ko gidaje da zai bar mana (’ya’yansa)a matsayin gado, amma zai bar mu mu yi karatu zai kuma biya mana kudin makaranta. Sai ga shi kuwa wannan ilimin da ya ba mu yana amfanarmu. Domin duk abin da muka zama ko muka samu a rayuwa ta dalilin wannan ilimin ne. Haka su ma iyayenmu mata sun taimaka mana wajen tarbiyyarmu da kula da rayuwarmu har muka kai inda muke a yanzu.
Haka kuma a kullum ina kallon nasarar da na samu a rayuwa, ta samu ne daga bangaren  maigidana saboda irin dimbin gudummawar da ya ba ni a rayuwa, tun daga lokacin da nake karatuna a jami’a har zuwa yanzu. Duk abin da na zo masa da shi matukar bai saba wa addini ko al’ada ba to zai amince tare da ba ni goyon baya dari bisa dari.
Haka ita ma abokiyar zamana wacce nake daukarta a matsayin babbar yayata, kuma babbar kawa, domin ta taimaka min kwarai da gaske musamman wajen kula min da yara a duk lokacin da wani aiki ya taso min. Haka kuma takan ba ni shawarwari akan lamurrana.
kalubale:
Duk da cewa rayuwa ba yadda za a ce babu kalubale, amma zan iya cewa babu wani kalubale a rayuwa da ya gigita ni ko ya sa na kasa samun mafita ba. Wannan kuwa ya samu ne ta hanyar abokan zama na arziki da muke da su.  Kowane mataki na rayuwa akwai irin nasa kalubalen, sai dai kowane irin kalubale a rayuwa yakan zo ya wuce.
Ayyukan da nake yi a Ma’aikatar mata:
Ita wannan gwamnati ta Dokta Abdullahi Ganduje yana son kulawa da harkokin mata. Tunda na shiga wannan ofis babu abin da muka taba kai wa gaban Gwaman wanda na ci gaban matan jihar ne ba tare da ya yi farin ciki tare da sanya albarka ba. Kullum burin Gwaman shi ne yadda za a samu matan Kano su zama masu dogaro da kansu ta yadda za su rika samun kudin shiga. A yanzu haka mun bijiro da ayyuka daban daban, akwai shirinmu na Kano kal-kal. Wannan shiri na kwasar shara ne wanda muke so mu bai wa mata motocin kwasar shara inda za su rika bi gida-gida suna kwasar shara ana ba su ladan aikinsu wanda bai wuce Naira 20 a duk gida ba. Matan nan da kansu za su tuka motocin kwasar sharar bayan mun koya musu tuki. Da farko za mu fara ba su motocin a matsayin bashi. Idan mun ga mace tana da kokari za mu taimaka mata ta hanyar hada ta da  kananan bankuna (micro finance)  wadanda su a shirye suke su taimaka musu. Anan za mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya; mun sama wa mata sana’a sannan a gafe guda kuma an tsafatace jihar. Muna sa rai mata su zama silar raba Kano da shara. Haka kuma mun bullo da shirin koya wa mata aikin kanikancin mota yadda za a samu garejin gyaran mota na mata zalla a cikin Jihar Kano insha Allah. Haka kuma a yanzu haka mun fito da wani shiri na yadda za mu ga mun kula da rayuwar mata da ke kurkuku, muna kokarin ganin sun sami duk abinda ya kamata su samu na kulawa. Haka  kuma muna kokarin koya musu sana’o’i.
Akwai gidan da ake ajiye kananan yara da suka aikata laifi wanda mu muke kula da su, kuma a kullum kokari muke mu ga yadda za mu kyautata rayuwarsu.
A yanzu haka muna kokarin farfado da cibiyoyin ci gaban mata da ke kananan hukumomi, ta yadda matan da ke kauyuka za su samu tallafin gwamnati, za a koya musu sana’o’i tare da ba su dan jari da za su fara sana’o’i. Idan matan nan suka samu haka ba sai sun shigo birni neman aikatau ko sana’a  ba. Abu na gaba kuma shi ne yadda za mu bunkasa wa matan kasuwa, ta yadda za su rika shigar da kayayyakin da suka sana’anta. Mun lura cewa duk yadda mutum ya kai da yin sana’a idan bai samu kasuwa ba, to abin ba zai ci gaba ba.
Haka kuma idan aka dauki batun fyade muna kokari wajen ganin mun wayar wa mata kai yadda za su kula da ’ya’yansu  tun farko. Muna nuna musu irin matakin da ya kamata su dauka da zarar irin hakan ta faru (Allah ya kiyaye). Haka kuma muna nuna musu amfanin fitowa su bayyana batun, a maimakon rufe maganar da ake yi, wanda a wasu lokutan yake kawo matsala ga ’ya’yan, musanmman ta fuskar abin da ya shafi lafiyarsu.
Saboda yadda wannan gwamnati ta damu  da harkar fyade a jihar nan a yanzu haka ta tsaurara hukuncin fyade, daga shekaru 40 a kurkuku zuwa hukuncin daurin rai-da rai  kai har ma da kisa. Har ila yau muna kokari mu ga mun kawo karshen harkar shaye-shayen muggan kwayoyi a jihar nan. Bincike ya nuna cewa matan jihar kano sun shiga harkar nan ta shaye-shaye sosai a daya bangaren kuma ga matasa wanda da ma sun dade a cikin wannan mummunan al’amari.  Muna da cibiyar gyaran halayyar  matasan a garin kiru wacce muke ajiye su muna kokarin ganin yadda za mu dawo da su cikin al’umma. Zan yi amfani da wanann dama wajen yin kira ga jama’ar Jihar Kano musamamn wadanda suke da irin wadanan matasa da su kawo mana su. Mun gama shirya komai a wanann cibiya sai dai saboda rashin yaran a hannunmu ya sa har yanzu ba mu fara gudnar da aiki a wurin ba. ’Ya’yan da ke hannunmu sun yi kadan a bude wurin, don haka muke kira ga duk iyayen da suka san suna da irin wadanann ’ya’yan su kawo mana su.
Burinta:
Babban burina shi ne na gama wannan aiki da aka dora min lafiya. Haka kuma ina burin na ga na cika da imani.
Abin da take son bari a bayanta:
A yau ina fatan na ga cewa na gudanar da wasu ayyukan taimaka wa al’umma musamamn ma ’yan uwana mata. Ina so  na yi ayyukan da ko bayan ba na nan za a tuna da cewa an taba yin wata Kwamishinar mata a Kano, wacce ta yi ayyukan taimakawa al’umma.
Mutane abin koyi:
A gaskiya irin wadanan mutane suna da yawa. Na farko maigidana shi ne babban abin koyi a wurina. Yadda yake gudanar da rayuwarsa abin koyi ne a wurina. Haka kuma Gwaman Kano Dokta Abdullahi Ganduje game da yadda yake da kyawawan manufofi game da ci gaban rayuwar mata.
Shawarwari ga mata:
Babbar shawarata ga ’yan uwa mata ita ce duk matar da take da aure ta yi kokari wajen rike aurenta da daraja. Kada ta yi wasa da sauke nauyin da ke kanta na mijinta a kowane irin yanayi ta samu kanta. Haka kuma tarbiyyar ’ya’yanta, kada ta yarda wani abu ya dauke mata hankali game da kula da tarbiyyar ’ya’yanta. Kowane irn aiki ko sana’a take ta sa gidanta a gabanta. Kada ta yarda ta yi wasa da tarbiyyar ’ya’yanta. Sannan kuma ga wadanda ba su yi aure ba su kama kansu, a duk lokacin da mace ta kame to za ta fi samun miji nagari. Wannan banzatar da kai da wasu matan ke yi ba shi ne zai sa su samu mijin aure musamman nagari ba.
Ina kira ga mata da su tsaya su nemi sana’a. kada mace ta zauna ta dogara ga mijinta. Mun san cewa a addinance dukkanin hakkin mace yana kan mijinta, amma saboda yanayin rayuwa da ake ciki  ya sa dole sai mace ta nemi nata, ko don ta tallafa wa mijinta da ’ya’yanta. Shi ma mijin yana bukatar tallafi. Ba komai ne za ki  rika nema a wurin mijinki ba. Idan ya kasance kina da sana’a za ki ga ko zaman auren ya fi karko.
Sannan ina kira ga mata wadanda suka sanya kansu cikin harkar shaye-shaye da su taimaki kansu su daina. A matsayinki na mace mai bayar da tarbiyyar idan kina shaye-shaye me kike so ’ya’yanki su koya daga gare ki. Mata ku sani cewa shaye-shaye ba ya kawar da bakin cikin rayuwa, mafita ita ce addu’a kawai.  Ina kira ga maza da su rika kula da matansu da zarar sun ga wasu canje-canje daga gare su  kamar yawan bacci da sauransu. Da zarar sun gano irin wadnanan abubwa sai su gagaguta daukar mataki tun kafin al’amarin ya yi zurfi yadda sai an sha wahala kafin ta daian ko kuma ma a kasa shawo kan matsalar.