Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano da Tashar Talbijin ta Arewa24 sun yi sulhu kan takaddamar da ta taso kan nuna fim din Kwana Casa’in.
Shugaban Hukumar, Malam Isma’ila Na’abba Afakalla ne ya bayyana haka a sakon da ya fitar a makon jiya.
A cewarsa, “Bayan zama da aka yi tsakanin Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano da jami’an tashar talabijin ta Arewa24 jiya, an kai ga matsaya inda aka amince za a cire bangarorin da suke dauke da abubuwan da al’umma ke korafi a kansu.”
Ya kara da cewa tashar talabijin ta Arewa24 ta amince cewa nan gaba ba za ta sake nuna wani fim din Hausa ba sai “ya kasance wanda yake da shaidar tantancewa da ta fito daga Hukumar Tace Fina-Finan.”
A makon jiya ne hukumar ta fitar da sanarwar dakatar da ci gaba da nuna shirin na Kwana Casa’in da shirin Gidan Badamasi wadanda suka yi tasiri sosai ga dimbin masu kallo a sassan duniya.
Malam Isma’ila Na’abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa fina-finan biyu sun ci karo da tsarin dokokin hukumar, inda ya ce a shirin Kwana Casa’in an nuna maza suna cacumar wata yarinya. A shirin Gidan Badamasi kuma ya ce an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, wadanda dukkansu a cewar Afakallah sun saba wa sashi na 102 na dokar da ta kafa Hukumar Face Fina-Finai ta Jihar ta shekarar 2001.
Shirin Kwana Casa’in wasu kungiyoyi na duniya da hadin gwiwar Gidauniyar MacAurther ne ke daukar nauyinsa, yayin da Falalu Dorayi ne furodusan shirin Gidan Badamasi.
Labarin dakatar da shirye- shiryen bai yi wa dimbin masu kallo dadi ba, inda ake ganin babu wani shiri da ake yawan kallo da ake nunawa a wata kafar talabijin a Arewacin Najeriya kamarsa. Sai dai wadansu sun yaba dakatar da shirin inda suka ce yana nuna wasu al’adu da suka saba wa al’adun Hausawa da addinisnsu.
Shirin Kwana Cas’in ya shafi siyasa da kuma ban kado yadda rashawa ta yi katutu a harkokin gwamnati. Kazalika shirin na nuna irin yadda wadansu talakawa suke da hadama da rashin gaskiya a mu’amalarsu ta yau da kullum.