Kwamitin SBMC na Makarantar Firamare ta Adamu Dikko da ke Tudun Jukun ya shawarci al’umma da kada su bar wa gwamnati kula da harkar ilimi ita kadai.
Kwamitin SBMC din ya yi wannan kira ne lokacin bikin kaddamar da gidaje shida tare da sanya sunayen wadansu fitattun mutane da suka shahara wajen tallafa wa harkar ilimi a yankin.
Gidajen da aka kaddamar su ne Liman Usman wadda shi ne ya samar da filin da aka gina makarantar kyauta ga al’ummar unguwar lokacin da gwamnati ta nemi inda za ta gina makarantar, sai gidan Yusuf ’Yan Bita da Mu’azu Bawa da kuma Albabello da kuma gidan tsohon dalibin makarantar Hanan.
Da yake kaddamar da gidajen Sakataran Ilimi na Karamar Hukumar Zariya Alhaji Mukhtar Maude, ya bayyana jagororin SBMC da kungiyar iyaye da malamai na makarantar da cewa jajirtattu ne masu himma da hangen nesa.
Ya ce al’ummar Tudun Jukun sun nuna cewa harkar ilimi ba ta gwamnati ce ita kadai ba saboda haka ya bayyana kudirinsa na ganin makarantun firamare na Karamar Hukumar Zariya sun samu ci gaba da ake bukata.
Sakataran Ilimin ya bukaci makarantu da ke Zariya su hanzarta tsara nasu kamar yadda Makarantar Adamu B. Dikko suka yi. Ya kuma yi alkawarin sanya kofi domin makarantun firamare na gwamnatin su yi gasa a tsakaninsu.
A sakon Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Alhaji Aliyu Idris Ibrahim ta hannun Rilwan Abubakar mai ba shi shawara kan watsa labarai da sadarwa ya taya shugaban makarantar murnar wannan ci gaba da suka yi tunanin samarwa don ci gaban dalibai.
Ya bayyana cewa, Karamar Hukumar Zariya ba da jimawa ba za ta aiwatar da nata aikin a makarantar don inganta harkar karatu da koyarwa.
Tun farko a jawabin maraba, Shugaban Kwamitin Gudanarwar SBMC, Alhaji Saleh Mowarki (Mai Unguwa) ya yi kira ne a samar da karin dakunan karatu domin wadanda ake da su sun yi kadan kuma sun tsufa.
Alhaji Saleh Mowarki ya kuma bukaci iyaye su rika karfafa wa kwamitin gwiwa don ci gaban makarantar.