A ranar 19 ga Satumba ne ayarin wakilan Kwamitin Shugaban kasa kan Arewa maso Gabas (PCNI) ya mika wa Gwamnatin Jihar Bauchi kayayyakin tallafi da suka kunshi abinci da sauransu.
Ayarin na karkashin Injiniya Mohammed Gambo Umar wanda ya wakilci Shugaban Kwamitin Laftana Janar T.Y. danjuma (mai ritaya). A jawabinsa Injiniya Umar ya gode wa gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi kan kaunar da suke nuna wa ’yan gudun hijira da rikicin Arewa maso Gabas ya raba da muhallinsu. Ya ce duk da cewa babu sansanin da aka ajiye ’yan gudun hijira a Bauchi, jihar ta yi fice wajen kyakkyawar tarba da karbar ’yan gudun hijirar inda dubbai suke zama da su a gidajensu kuma suke ba su gonaki tare da cin gajiyar asibitoci da makarantu da sauran kayayyakin jin dadin rayuwa da sauran mutanen jihar.
Ya yaba wa kokarin Gwamnatin Jihar Bauchi kan rungumar ’yan gudun hijirar tare da ba su filayen yin noma da sauran kayayyakin bukatu duk da karancin kudin da jihar ke da shi. Ya ce Jihar Bauchi tana taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Kwamitin PCNI sakamakon rungumar baki da yadda take karbar dimbin ’yan gudun hijirar da ke kwarara jihar.
Injiniya Umar ya ce Kwamitin PCNI ta hannun karamin Kwamitin Bunkasa Tattalin Arziki, wanda shi wakili ne, ya tsara dimbin shirye-shirye a bangaren aikin gona da koyar da sana’o’i da inganta rayuwar mata da yara da samar da hanyoyi da gyara asibitoci da makarantu da sauran ayyukan inganta tattalin arziki da rayuwa don kawo sauki ga mutanen yankin.
Ya yi kira ga jihar ta ci gaba da bayar da hadin kai.
Kayayyakin da kwamitin ya mika sun hada da buhunan shinkafa masu girman kilo 25 guda 2000 da buhunan masara da gero da kuma buhunan sukari masu nauyin kilo 50 guda 1,500 da buhunan wake 1,500. Sauran sun hada da kwanon rufi 1000 da kayayyakin aikin abinci 3000 da katifu da filo 400 da buhunan siminti 5000 da katakai masu inci 12 guda 1000 da kuma bokitan fenti 4000.