A ranar Litinin da ta gabata ce, Kwamitin Shugaban kasa kan Arewa maso Gabas (PCNI) ya karbi muhimman magunguna daga kamfanin harhada magunguna na BCN Pharmaceutical domin tallafa wa ’yan gudun hijira.
Magungunan da aka mika a ofishin kwamitin da Mataimakin Shugaban Kwamitin, Alhaji Tijjani Tumsah ya karba a madadin Shugaban Kwamitin Laftana Janar T.Y. danjuma (mai ritaya), sun hada da katan 10 na maganin ruwa na Febrilid mai nauyin milimita 60 da katan 10 na maganin ruwa na Junibite milimita 100 da katan 10 na Ibad, Suspesion milimita 60 da katan biyu na kwayoyin magani na Beecoodeen da katan 10 na Paracetamol da katan 10 na man Calamins milimita 10 da katan 10 na maganin Nerbe and Bone milimita 180 da katan 10 na maganin shaka na Penetrol Inhalant milimita 10.
Alhaji Tumsah ya gode wa kamfanin kan jin kai dan Adam da suka nuna inda ya yi musu alkawarin za a isar da magungunan ga wadanda aka yi niyyar su ci gajiyarsu. Ya ce Kwamitin PCNI yana duba hanyar kara hadin gwiwa da kamfanin.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Shugaba kuma Babban Jami’in Zartarwar Kamfanin BCN, Alhaji Ahmed Yusuf Ahmed ya ce Kamfanin Harhada Magunguna na BCN Pharmaceutical kamfani ne da ke saurin bunkasa a Najeriya tare da samun yabo a duniya. Ya ce, Kamfanin BCN ya yanke shawarar hada hannu da Kwamitin PCNI don magance matsalolin kiwon lafiya a sansanonin ’yan gudun hijira da ke yankin Arewa maso Gabas. Ya yi alkawarin cewa Kamfanin BCN zai hada hannu da Kwamitin PCNI wajen samar da kayayykin kiwon lafiya tare da samar da mafita a yankin a duk lokacin da aka bukaci haka.