Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) ya fara gudanar da aikin duba lafiya kyauta ga ’yan gudun hijira dubu 15 a garin Mubi da ke Jihar Adamawa. Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI, Alhaji Tijjani Tumsah ne ya sanar da haka a wajen kaddamar da shirin a Babban Asibitin Mubi a ranar Juma’a da ta gabata. Alhaji Tumsah ya ce shirin na cikin Shirin Shugaba Muhammadu Buhari na tabbatar da kiwo lafiya ga marasa galihun ’yan gudun hijira da mazauna garuruwan da sansanonin gudun hijirar suke.
Da farko an tsara shirin ne domin ’yan gudun hijira 5,000 daga kananan hukomomi bakwai da suka fi shiga cikin rikici a jihar, amma saboda yadda mutanen da ke bukatar tallafin kiwon lafiya suke tururuwan zuwa, sai aka fadada shirin.
A cewar Mataimakin Shugaban Kwamitin, za a yi kwana bakwai ana gudanar da shirin a jihar, kuma shirin zai shafi mutane daga kananan hukumomin Madagali da Michika da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu da Maiha da Hong da kuma Gombi. Ya ce an riga an yi irin wannan shirin a Borno da Yobe, inda ya bukaci gwamnonin jihohin da aka gudanar da irin wannan shiri su ci gaba da shirin ga al’ummomin yankin.
Babban Daraktan kungiyar ProHealth Internationl, Dokta Iko Ibanga ya ce ma’aikatan lafiya 80 ne suke aiki a karkashin shirin. Dokta Ibanga ya ce wadanda za su ci moriyar shirin, za a duba lafiyarsu ne a bangarorin cututtukan da suka zama ruwan dare kamar ciwon ido da kananan yara da awon ciki da bayar da magunguna da duba hakura da tiyata.
Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa ya yi godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan tallafi, sannan ya tabbatar da cewa masarautarsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga duk wani shirin tallafi na gwamnati.