✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin PCNI ya fara bayar da horo kan tabbatar da adalci

Kwamitin Shugaban Kasa kan Sake Gina Arewa maso Gabas ya fara gudanar da shirin bayar da horo kan gina zaman lafiya da tabbatar da adalci…

Kwamitin Shugaban Kasa kan Sake Gina Arewa maso Gabas ya fara gudanar da shirin bayar da horo kan gina zaman lafiya da tabbatar da adalci a tsakanin al’umma a garin Maiduguri da ke Jihar Borno.

Taron wanda aka fara gudanar da shi tun ranar  Litinin, 5 ga watan Nuwamba ya samu halartar sarakunan gargajiya da alkalai da shugabannin addini kuma an shirya taron ne don a basu horo kan yadda za su kware wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma kokarin baiwa kowa damar samun adalci a garuruwansu.