Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta.
Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.”
- Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio
- Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi
A ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci.
Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu, don haka majalisa ba ta da ikon yin hukunci a kansu.
Yadda Rikicin Ya Samo Asali
A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata.
Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru.
Abin da Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisa
Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafinta ga Majalisar Dattawa, inda ta ce: ’Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi na lalata da kuma amfani da muƙaminsa wajen tauye min haƙƙi na ’yar majalisa.”
Daga nan sai ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna sannan ta ajiye takardun ƙorafinta.
Shugaban Majalisar, Sanata Akpabio, ya karɓi ƙorafin, inda ya miƙa shi ga Kwamitin Ladabtarwa da Tsare-Tsare domin gudanar da bincike.
Ta ce: “Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa domin yin bincike kuma su dawo mana da rahoto cikin gaggawa.”
Duk da haka, yayin da ake tattaunawa, Babban Mai Tsawatarwa na Majalisa, Sanata Mohammed Monguno, ya ce ba za a iya tattauna ƙorafin ba saboda yana da nasaba da shari’ar da ke gaban kotu.
Sai dai Sanata Natasha ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa ƙarar da ake yi a kotu ba ta shafi ƙorafin da ta gabatar ba.
Ta bayyana cewa abin da ke gaban kotu na da nasaba da wani hadimin Akpabio, Patrick Mfon, wanda ya zarge ta da sanya kayan wanda ba su dace ba a majalisar.
Martanin Sanata Akpabio A Kan Zargin
Bayan karɓar ƙorafin, Akpabio ya musanta duk wasu zarge-zarge da Natasha ta yi masa.
Ya ce: “Dangane da zargin da ake yi min, babu lokacin da na taɓa yunƙurin cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace.
“Mahaifiyarmu ta ba mu tarbiyya tun muna ƙanana, kuma ni ma ina da ’ya’ya mata huɗu. Bugu da ƙari, lokacin da nake gwamna, an taɓa karrama ni a matsayin gwamnan da ya fi kowa girmama mata.”
Akpabio ya kuma jaddada cewa lamarin na gaban kotu, don haka ya buƙaci kafafen watsa labarai da al’ummar Najeriya su jira sakamakon shari’a.
’Yan Majalisa Ba Su Goya Wa Natasha Baya Ba
Bayan gabatar da ƙorafin, mafi yawancin ’yan majalisar dattawa da suka yi tsokaci ba su goyi bayan Natasha ba, har da sanatoci mata ’yan uwanta.
Wasu daga cikinsu sun ce ƙorafin ba shi da tushe, don haka bai kamata a tattauna shi a zauren majalisar ba.
Wasu kuma sun nemi a yi zaman sirri domin tattauna lamarin, amma Akpabio ya ƙi amincewa da hakan saboda akwai baƙi da suka ziyarci majalisar daga Birtaniya, don kallon yadda majalisar ke tafiyar da lamarin.