Kwamishinan Raya Karkara da Birane na Jihar Zamfara, Abubakar Abdullahi ya dauki nauyin aurar da mata zaurawa 50 a Karamar Hukumar Tsafe.
A jawabinsa a wurin daurin auren da aka gabatar a Fadar Sarkin Tsafe ranar Asabar, Abdullahi ya ce daukar nauyin aurar da zawarawan wata dama ce ta karfafa guiwar masu rauni da rangwame a cikin al’umar da ayyukan ’yan ta’adda suka rutsa da su.
- Najeriya ta kashe $6bn wurin shigo da alkama —Minista
- Bakuwar cuta ta kashe mutum 20 a Binuwai
- ’Yan aji dayan sakandare a Kano za su koma makaranta ran Litinin
Kwamishinan ya jinjina wa Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa da malaman Islama na yankin da suka karfafa masa guiwa kan daukar nauyin auren.
“Daukar nauyin auren ya zo daidai da kudurin gwamnati mai ci ta Gwamna Bello Matawalle na magance matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar”, inji shi.
A jawabinsa, Gwamna Matawalle ya yaba wa kwamishinan bisa kokarinsa na daukar nauyin auren.
Matawalle, ta bakin Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Nasiru Magarya ya bukaci jami’an gwamnatin jihar da ’yan siyasa su dabi’antu da taimakon raunana da mabukata don sanya musu farin ciki.