✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwamandan ISWAP ya kashe mataimakinsa saboda harin da sojoji suka kai musu

A harin dai sojoji sun kashe matakan ISWAP 41

Wani Kwamandan kungiyar ISWAP, Abu Muhammed, ya kashe mataimakinsa, Abu Darda, bisa laifin yin sakacin da ya kai sojoji suka kai musu hari suka karkashe masa mayaka a sansanoninsu.

An kai musu harin ne a sansanoninsu da ke kauyukan Mukdolo da Bonei wanda ya kai ga kashe mayaka 41, ciki har da Abu-Zahra Munzir.

A rahoton da aka tattaro cewa kwamandan da ya fusata ya kashe Abu Darda a gaban sauran mayakan a kauyen Kajeri Dogumba da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa Abu Muhammed ya zargi Abu Darda da jagorantar hare-haren da ba a yi nasara ba a ranar 19 ga watan Maris a garin Mafa wanda ya yi sanadin kashe ’yan ta’addan da dama tare da kama wasu makamai daga cikin motocinsu.

Kwamandan ya ce suna da manyan motoci uku ne kawai amma Abu Darda ya yi sakacin da har sojojin Najeriya suka samu nasarar kama su.

Ya ce bai iya waiwaya bayansa ba yayin da har sojoji suka bi sawunsa suka far musu a sansaninsu a lokacin da suke barci suka kai ga kama motocin.

Kwamandan ya ce ya ji zafi musamman saboda sojoji sun kashe mayakansa da dama, sun kona masa kayan abincinsa da wasu sabbin kayan da aka sayo domin bikin auren da suke shirin yi.

Kwamandan wanda a halin yanzu yake tara mayakansa a Kajeri Dogumba, Bula Yagana Aliye a Karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno, ya sha alwashin daukar fansa kan kashe mayakan nasa da sojojin suka yi.

Dakarun sojojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai, sun kai farmaki maboyar kungiyar ta’adda ta ISWAP da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno, inda suka kashe 41 daga cikin ’yan ta’addan ciki har da kwamanda Abu Zahra.