✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalliyar da amarya ya kamata ta yi kafin ranar biki

Ranar bikin kowace ‘ya mace babbar rana ce a rayuwarta kuma a wannan ranar kowa yana son ya ga irin kwalliyar da za ta yi.…

Ranar bikin kowace ‘ya mace babbar rana ce a rayuwarta kuma a wannan ranar kowa yana son ya ga irin kwalliyar da za ta yi. Koda ’yan gidan amaryar ne suna son kare mata kallo a wannan ranar. Wasu amaren tsabagen son gyaran jiki har gyaran ya yi yawa ya feso musu da kuraje a fuska ko da ba su da wadannan kurajen. Don haka ne a yau muka kawo muku yadda amaryar gobe za ta kimtsa kanta kafin ranar biki.
• Amaryar gobe ta kasance tana yawan shan ruwa, sirrin hakan shi ne kar jikin ya yankwane. Kuma yana da kyau ta kasance mai shan kankana sosai, domin gyaran fatar jikinta da kuma cin su latus da ‘ya’yan itatuwa.

• Ana son amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura watanni uku. Ta san irin mayukan da za ta shafa da kuma irin abincin da za ta ci.

• Idan amaryar gobe ta wuce shekaru 20, yana da kyau tana kwaba fiya da zuma tana shafawa a fuskarta domin warkar da kananan kurajen fuska kafin ranar biki.

• Idan shekarunta sun wuce 25, yana da kyau ta kasance cikin yin dilke, domin cire dattin fuska. Kuma hakan na rage mata shekaru a fuskanta.

• Yana da kyau ta sayi magungunan turawa na gyaran jiki (supplement). Wadannan magungunan na dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma na omega3, wanda aka fi samu a man kifi. Wadann magungunan na sanya fata sulbi da laushi.

• A samu mai mai kyau tsayayye, wanda za a rika shafawa na tsawon wadannan lokuta. Ana shafa wannan nau’ukan man a kalla sau biyu a rana.

• Yana da kyau amaryar gobe ta samu lokacin yin bacci sosai, kuma ta rage shiga rana domin gyaran fata da kuma hutu.

• Tana amfani da soson hoda mai tsafta ba mai datti ba, domin rage haifar da wasu kurajen fuskar.

• Domin samun fata mai haske a samu kurkum da ruwan lemun tsami da kuma man zaitun kamar rabin cokali karami da madara sannan ta shafa a fuskanta na tsawon rabin awa, sannan ta wanke.
A kullum za ta rinka yin hakan safe da yamma lallai za a ga canji.