✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalejin koyon tukin jirgin sama ta Zariya ta sake zama wacce ta fi kowacce a duniya

Tun 2015 dai makarantar take samun kyautar a duniya

Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO) ta sake bayyana Kwalejin Koyon Tukin Jirgin Sama (NCAT) da ke Zariya a Jihar Kaduna a matsayin wacce ta fi kowacce a duniya.

Sakatare-Janar na hukumar, Juan Carlos Salazar, wanda ya gabatar da kyautar ga makarantar a birnin Istanbul na kasar Turkiyya ranar Laraba ya ce ta ciri tuta wajen horar da kwararrun matukan jirgin sama tsawon shekaru.

Carlos ya ce hukumar za ta ci gaba da tallafa wa kasashe mambobinta wajen cim ma burikansu, tare da jinjina wa kokarin Gwamnatin Tarayyar Najeriya wajen sake inganta harkar sufurin jiragen sama a kasar.

Tun shekarar 2015 dai hukumar ta ICAO take ba makarantar shaidar zama wacce ta fi horar da kwararun ma’aikatan jirgin sama mafiya yawa a duniya, da kuma wacce ta fi yawan kwasa-kwasan da hukumar ta amince da su a tsakanin sauran kasashe.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana kyautar a matsayin wata ’yar manuniya kan irin ayyukan da gwamnati mai ce ta yi wajen bunkasa fannin tun da ta hau kan karagar mulki.

Ya kuma yaba wa hukumar saboda la’akari da ci gaban da makarantar da ma harkar sufurin ke samu wajen bayar da kyautar.

%d bloggers like this: