Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta Najeriya (NDA) da ke Kaduna, ta bude shafin sayar da fom ga dalibai masu sha’awar neman gurbin karatu a fannin aikin soji karo na 73.
Magatakardan Kwalejin, Birgediya Ayoola Aboaba ya ce an bude shafin tun a ranar 23 ga watan Janairu zuwa 24 ga watan Afrilun 2021 domin masu sha’awar samun gurbin daukan horo a fagen aikin soji.
- Chelsea ta kori kocinta Frank Lampard
- Dara ta ci gida: An yi garkuwa da shugaban ’yan bindiga
- Mutum 6 sun mutu, 3,000 sun tsere bayan harin ’yan bindiga a Neja
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
Ya ce, “Masu sha’awar samun gurbi a Kwalejin na iya shiga shafinta na yanar gizo, rcapplications.nda.edu.ng, su zabi rukunin sayen form sannan su biya N3,500 kacal ta hanyar amfani da tsarin biyan kudi na REMITA.”
“A lura cewa wadanda suka biya kudin ta hanyar samun lambobin REMITA na ‘RRR’ da aka turo daga shafin namu kadai ne za mu karba,” a cewarsa.
Birgediya Ayoola, a cikin sanarwar ta ranar Lahadi, ya ce mata da kuma maza ’yan Najeriya da suka cancanci samun gurbin karatu a NDA na iya nema.
Magatakardan ya bukaci masu neman samun gurbin karatu a NDA da su sauke dukkanin ka’idodin da aka wallafa a shafin sannan su yi musu karatu na natsuwa.
Ya kuma ce masu neman gurbin su tabbata sun sanya kwalejin a matsayin zabinsu na farko yayin rajistar rubuta jarrabawar neman gurbin karatu a manyan makarantu ta JAMB.
Sannan kuma su tabbata sun samu mafi karancin makin da ake bukata a dukkannin kwasa-kwasai na digiri da ake gudanarwa a kwalejin.