✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwale-kwale ya sake kifewa da fasinjoji a Adamawa

Wannan na zuwa kwana biyu kacal bayan da hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin fasinjoji da dama a jihar.

Wani kwale-kwale makare da fasinjoji ya kife a garin Gurin da ke Karamar Hukumar Fufore a Jihar Adamawa.

A cewar wata majiya, wadanda abin ya rutsa da su galibi mata ne da kananan yara, wanda suke kan hanyarsu ta dawowa daga gona da bikin suna a lokacin da kwale-kwalen katakon ya nutse.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Adamawa, Dokta Mohammed Suleiman, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dokta Suleiman ya ce lamarin ya faru ne da tsakar ranar wannan Litinin din kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Fufore/Gurin a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Umar Bobbo Ismail, shi ma ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Wannan na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da mutum takwas suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a Rugange da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu a Adamawan.

Wani mazaunin yankin, ya ce za a iya hana aukuwar lamarin idan fasinjojin suna amfani da rigar ceto tare da bin da wasu matakan kariya.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da kula da magudanan ruwa a kai a kai da kuma samar da na’urorin kariya irin su rigunan ceto domin hana aukuwar hakan a gaba.

Hatsarin kwale-kwalen ya haifar da damuwa game da harkar sufurin ruwa, musamman a lokacin damina a yankin.